✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mamallakin gidan talabijin na AIT, Raymond Dokpesi, ya mutu

Mamallakin gidan talabijin din nan mai zaman kansa na AIT, Cif Raymond Dokpesi, ya mutu.

Mamallakin kamfanin Daar Communication masu gidan talabijin din nan mai zaman kansa na AIT da gidan rediyon Raypower, Cif Raymond Dokpesi, ya mutu.

Dan marigayin, Raymond Dokpesi (Karami) ne ya tabbatar da sanarwar a cikin wata sanarwa ranar Litinin.

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan mutuwar, amma iyalan mamacin sun yi alkawarin fitar da cikakkiyar sanarwa a kai nan ba da jimawa ba.

Sanarwar ta ce, “Cikin nuna alhini da jimami muke sanar da mutuwar Cif Raymond Dokpesi, wanda ya mutu ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023. Marigayin uba ne na gari, miji, mahaifi, kaka kuma aboki ga mutane da dama. Za a dade ana kewarsa.

“Marigayin fitaccen dan kasuwa ne kuma wanda ya mayar da hankali wajen kafafeb yada labarai, wanda ya sadaukar da ilahirin rayuwarsa wajen hidimta wa jama’a.

“Nan ba da jimawa ba iyalansa za su fitar da cikakkiyar sanarwa a kan rasuwar tasa,” in ji sanarwar.