Wani ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya ya hana kammala bukukuwan gasar ninkaya da bankin Zenith ga shirya wa makarantun firamare a Jihar Legas.
Gasar dai, wacce daya ce daga cikin hanyoyin bunkasa ninkaya a Najeriya na dab da farawa ne a filin Ikoyi Club kafin ruwan ya fara sauka.
- Ebonyi ta fice daga fafutukar kafa kasar Biyafara – Gwamna Umahi
- NAJERIYA A YAU: Yadda Dokar Zabe Ta Tantance Daliget
A cewar Shugaban shirya ninkayar, Kunle Adeniji, “Tilas ta sa muka dauki wannan matakin ba don muna so ba, sai don kiyaye lafiyar masu fafatawa a cikinta da kuma tabbatar da yin adalci.”
Ya ce nan ba da jimawa ba za a sanar da ranar da za a kammala gasar.
Shi ma Shugaban Kungiyar Masu Wasanni a Ruwa ta Najeriya, Babatunde Fatayi-Wiliams ya ce an dauki matakin ne bisa la’akari da dokokin kasa da kasa.
Jimillar makarantun firamare 14 ne suke fafatawa a gasar da masu ninkaya 226.
Adeniji ya kuma yaba wa bankin tare da dukkan masu shirya gasar da makarantun da suka fafata a ciki saboda hadin kan da suka bayar har ta samu nasara.