✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mama Dinah A. Kashere: Mu kula da karatun mata

Mama Dinah A. Kashere, shahararriyar manomiya ce kuma gogaggiyar ’yar siyasa wacce ta ga jiya ta ga yau, kuma har yanzu ana damawa da ita…

Mama Dinah A. Kashere, shahararriyar manomiya ce kuma gogaggiyar ’yar siyasa wacce ta ga jiya ta ga yau, kuma har yanzu ana damawa da ita a siyasar jihar domin ta yi takarar mukamai daban- daban kama daga kan kansila, ’yar majalisar jiha da sauransu tun farkon dawowar siyasa a 1999, sannan kuma tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati ce wacce ta taka rawa sosai a vangaren aikin gwamnati domin ta fara aiki daga kan akawu har ta kai ma’aji ta karamar hukuma. 

Tarihin rayuwata
Sunana Mama Dina A. Kashere, ni ce Uwar Soron Tangale ta fari, kuma Sarauniyar Noman jihar Gombe ta fari, ni ’yar kabilar Tangale ce daga karamar hukumar Villiri a jihar Gombe. Amma an haife ni ne a garin Tasha da ke jihar Kano a lokacin mahaifina yana yawon wa’azin bushara a ranar 8 ga watan Agustan 1942. Na fara karatu a makarantar firamare ta Kabo da ke jihar Kano a shekarar 1954 zuwa shekarar 1960 .Daga nan sai na tafi makarantar sakandare ta Kabo da ake kira Girls High School daga shekarar 1960 zuwa shekarar 1967 .Bayan na gama karatun sakandare sai na samu tafiya Jami’ar Ahmadu Belloda ke Zaria daga shekarar 1967 zuwa shekarar 1972. Na yi kwas na Clark sannan na wuce na yi Difloma a vangaren kananan hukumomi a tsakanin wadannan shekarun.
Aiki
Na fara aiki ne tun a Tangale Waja lokacin ana N.A (Native Authority)a matsayin akawu a karamar hukuma bayan wani lokaci sai na samu karin girma zuwa Akanta bayan da aka dawo da hedkwata ta bar Tangale Waja ta dawo Villiri Kaltungo sai aka ba ni mukamin Ma’aji ta karamar hukumar, da wannan mukami ne har na yi ritaya a shekarar 1985.
Nasara
A lokacin da nake aiki na samu nasara domin mu mata ba mu da yawa, kuma maza ba sa so su ga mun wuce su, sai ya zama samun karin girma yana yi mana wahala.Amma idan mace ta kaskantar da kai ta yi ladabi da biyaya ga manya takan samu karin girma wanda hakan ya sa ni ma na samu karin girma har na kai matsayin akanta.
kalubale
Akwai kalubale sosai domin a wancan lokaci samun mace ta yi karatu yana wahala ni ma na yi karatu ne saboda kasancewar mahaifina mai bushara ne yana yawon wa’azi ya kuma san muhimmancin karatun boko shi ne damar da na samu, bayan na gama karatun sakandare kuma Turawan Mission ba su so na tafi jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ba, domin suna ganin kamar idan na tafi makarantar gwamnati
zan lalace amma da hakan mahaifina ya bar ni na je.
Lambar yabo
An ba ni Sarauniyar Noman jihar Gombe da kuma sarautar Uwar Soron Tangale saboda gwazona ne.Domin Sarauniyar Noma sai an yi bikin wasan gona ne ake bai wa wanda ya fi kwazo kuma tun da aka ba ni har yanzu ba a sake bai wa wani ba, haka ma Uwar Soron Tangale.
Kamar lambar yabo ta OON ma an zave ni a cikin wadanda za a bai wa a can baya amma da aka tantance sai ban samu ba da yake da ma sai an yi zave sannan a tantance.
kungiyoyi da kasashe
Ni tsohuwar shugabar kungiyar NCWS ce ta yankin Tangale Waja wacce na yi shugabanci na kimanin shekaru goma sha biyar.Na sauka a shekara ta 2009, sannan Mamba ce a yanzu .
Ni ce shugabar kungiyarmu ta yare ta Dul Yamba ta Tangale, kuma shugabar zumuntar mata ta Wange da Bare, har ila yau kuma Ma’aji ta zumuntar mata ta Katangeren.
Na je kasashe biyu ne kawai, Isreal da London.
Yawan iyali
’Ya’yana biyar hudu maza, daya mace, maigidana kuma Allah ya yi masa rasuwa a hatsarin mota.
Abin da na ke so a a tuna ni da shi
Ina so ko bayan raina a rika tuna ni da jakadiyyar zaman lafiya. Saboda ina shiga ko’ina don in fadakar da jama’a muhimmancin zaman lafiya.

Tufafi
Kasancewa ta ’yar Arewa, kuma na tashi a gidan da yake da addini mahaifina mai bushara, ina son in ga mace tana sanya suturar kirki wacce za ta rika rufe ko’ina a jikin mace.Domin babu kyau a ce mace ta yi shiga irin ta rashin kunya mai bayyana tsiraicinta, hakan ba al’adarmu ta Arewa ba ce, kuma ba mutuncin ’ya mace ba ne.
Shawara ga iyaye
A matsayina na ’ya mace wacce karatunta bai yi zurfi sosai ba amma ta san muhimmancin karatu ,ina so in jawo hankalin iyaye da cewa karatun ’ya mace yana da matukar amfani don haka a bar ’ya mace ta samu ilimin zamani, wanda da shi ne za ta iya zama da mutane yadda ya kamata.Sannan kuma idan mace ta yi ilimi ta fi jin tausayin iyayenta a kan da namiji.Bahaushe ya gama magana da ya ce idan aka ilimantar da mace daya kamar an ilimantar da al’umma ne.Ka ga ashe idan iyaye suka bar ’ya’yansu mata suka yi karatu za a goga kafada da su a ko’ina a kasar nan.Kuma za su iya kai wa matsayin da wani da namiji bai kai ba.
A kuma guji dora musu talla, domin talla yana lalata tarbiyar yara a cikin sauki.Ta hanyar talla ne kawai ake iya samun cimma burin kawar da ’yan matancin mace cikin sauki, inda saurayi zai rude ta wajen saye abin tallan nata ya ba ta kudi ya ce ta same shi a waje kaza. Shi kuwa sai ya yi amfani da wannan dama ya yi lalata da ita.Saboda haka wannan bai dace ba iyaye a kula don Allah.