Wani fitaccen malamin addinin musulunci a garin Zariya, Mallam Magaji Kwagoro da aka fi sani da Dan Aljanna, ya koka bisa karin kudin kujerar aikin Hajji na bana da Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta yi.
Malamin wanda ya bayyana haka lokacin da ya ke zantawa da wakilin Aminiya a Zariya, ya ce yanke kudin ajiya da Hukumar NAHCON ta yi na Naira miliyan daya da rabi ya yi yawa matuka musamman idan aka yi la’akari da mawuyacin hali da al’umma ke ciki a yanzu.
- An shiga rudani bayan kotu ta tsige Kakakin Majalisar Bauchi
- Tinubu zai tafi Dubai taron sauyin yanayi ranar Laraba
A bayan nan ne dai Hukumar Alhazan ta kayyade Naira miliyan huda da rabi a matsayin kudin kujerar aikin Hajjin bana.
Hukumar ta kuma umurci dukkan rassanta na jiha da su fara karbar kudaden kafin a kayyade tartibin kudin da za a biya a wannan shekara.
Mallam Dan Aljanna ya yi nuni da cewa aikin Hajji ba yawon shakatawa ba ne, aiki ne na addini da aka wajabta shi ga dukkan Musulmi wanda ya sami iko.
Kan haka ne malamin ya ce ya kamata gwamnati ta shigo ciki sosai don ba da tallafi ga yadda ake gudanar da aikin saboda musulmi su samu sauki.
Ya kara da cewa, “in dai kudaden suka ci gaba da zama a haka ko kuma karuwa, babu shakka musulmi masu matsakaicin karfi ba za su samu damar sauke faralin su ba.”
Dan Aljanna ya ce aikin Hajji zai zamanto an bar wa manyan ma’aikatan gwamnati da manyan ’yan siyasa da kuma masu hannu da shuni, a yayin da wanda ba su da kunbar susa dole su hakura da gudanar da daya daga cikin rukunan addinin su.
Mallam Magaji ya roki gwamnati da wakilan al’umma na Majalisar Tarayya da su hada hannu wajen ganin an saukaka farashin kudaden aikin Hajjin.
Ya ba da shawarar cewa ’yan Majalisar Tarayya su kawo wani kudiri da zai tilasta wa gwamnati saka tallafi a aikin don saukaka kudaden da ake kashewa wajen neman kujera.
Dan Aljanna ya kuma roki masu hali da su ci gaba da taimaka wa al’umma wajen ganin an magance irin mawuyacin halin da ake ciki.
Dangane da batun matsi da al’ummar kasa ke ciki, malamin ya shawarci jama’a da a koma ga Allah kuma a ci gaba da addu’o’i don samun saukin lamarin.
Ya nanata bukatar a kara kaimi wajen rungumar sana’o’i komai kankantar su don samun abin dogaro da kai, yayin da yake rokon masu hali da su rika taimaka wa marasa karfi.