Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami, ya fasa neman takarar Gwamnan Jihar Kebbi inda zai ci gaba da rike mukaminsa na Minista a Gwamnatin Tarayya.
A baya dai an yi ta rade-radin cewa Ministan zai ajiye mukaminsa don ya tsaya takarar Gwamnan a karkashin jam’iyyar APC.
- Ganduje ya bi Shekarau har gida don kokarin ‘hana shi ficewa daga APC’
- Taliban ta wajabta wa mata sanya nikabi a Afghanistan
Ko a ranar Juma’a, an ayyana sunan shi a cikin wadanda suka halarci wani taron bankwana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shirya wa Ministoci 10 da ke shirin tsayawa takarar mukamai daban-daban.
A cewar wasu majiyoyin da ke da kusanci da Ministan, Malami ya yanke shawarar ci gaba da zama a matsayin Minista a maimakon tsayawa takarar Gwamnan.
A ranar Laraba ce dai Shugaba Buhari ya ba dukkan masu rike da mukaman siyasa da ke sha’awar tsayawa takara nan da ranar Litinin mai zuwa su sauka daga mukamansu, kamar yadda Dokar Zabe ta tanada.
Ana ganin Malami dai a matsayin daya daga cikin mutanen da suka fi karfin fada a ji a gwamnatin Buhari.