✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Malaman kwalejojin fasaha za su tsunduma yajin aikin gargadi

Kungiyar ta ce yajin aikin na gargadi ne

Kungiyar Malaman Kwalejojin Fasaha ta Kasa (ASUP) ta ce za ta tsunduma yajin aikin gargadi na sati biyu daga ranar Litinin.

ASUP ta bayyana haka ne ta bakin shugabanta, Anderson Ezeiba, bayan taron gaggawa da ta gudanar da bangaren zartarwarta ranar Laraba.

Shugaban ya kuma ce za su fara yajin aikin ne saboda kin biya musu bukatunsa da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Idan za a iya tunawa dai ko a ranar shida ga watan Afrilu da kuma 10 ga watan Yunin 2021, biyo bayan sanya hannun kan yarjeniyoyinta da Gwamnatin Tarayya tabyi, ASUP din ta dage tsunduma yajin aikin da ta kuduri aniya.

Yarjeniyoyin dai sun hada da biyan kungiyar Naira biliyan 15 na kudin farfado da makarantun da gwamnatin ta amince za ta biya, amma ta gaza yin hakan.

Haka kuma, akwai batun biyan bashin sabon tsarin albashin Gwamnatin Tarayyar na wata 10 da shi ma gwamnatin ba ta biya ba.

Sai kuma wani bangare na kudin manyan makarantun da suka kai Naira biliyan 19 da ke jiran sahalewa daga ofishin babban akanta na kasa.

“Muna rokon al’ummar Najeriya da su roki gwamnati da ta yi abinda ya dace a sati biyun nan domin dakatar da yajin aikin sai baba ta gani a gaba,” inji kungiyar.

Wannan dai na zuwa ne bayan kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta sake tsawaira nata yajin aikin da karin wata uku.