kungiyar Shugabannin Makarantun Firamare wacce ake kira AOPSHON ta yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa su gurfanar da duk wani ma’aikacin gwamnatin da aka samu da hannu a badakalar sanya sunayen malaman bogi a cikin jerin sunayen ma’aikatan jihohinsu.
Mataimakin sakataren kungiyar reshen jihohin Arewa, Kwamared Ya’u T.K Isa Tilde, shi ne yayin kiran yayin da yake tattaunawa da Aminiya ta wayar salula a karshen makon jiya.
Kwamared Tilde wanda ,har ila yau, shi ne sakataren kungiyar na Jihar Bauchi ya yaba wa wasu gwamnonin Arewa kan aikin tantance malaman jihohinsu da suke yi.
Ya ce tuni har wasu jihohin sun gano malaman bogi masu yawa wadanda ake zargin wasu ma’aikatan jihohin sun dauka aiki.
“Saboda haka muna kira ga gwamnoninsu kama tare da gurfanar da duk wani ma’aikaci da aka samu da hannu dumu-dumu a badakalar daukan malaman bogin aiki don ya zama darasi ga wadanda suke shirin aikata irin wannan danyen aiki nan gaba,” inji shi.
Ya ce samun malaman bogi badakala ce da ke shafar mutuncin kowace jiha a idanun duniya.
Ya bayyana takaicinsa dangane da irin yadda wasu ma’aikata marasa kishi suke daukar wadanda ba su dace da aikin malanta ba suna tura su makarantu firamare a yankin Arewa.
Ya ce irin wannan dabi’a tana rage kimar aikin malanta tare da gurgunta kokarin da gwamnati take yi wajen samar da ingantaccen ilimi.
Ya yaba wa gwamnan Jihar Bauchi saboda daukar matakan da suka dace wajen zakulo malaman bogi a jihar.
Malaman bogi: kungiyar AOPSHON ta nemi a hukunta ma’aikatan gwamnati
kungiyar Shugabannin Makarantun Firamare wacce ake kira AOPSHON ta yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa su gurfanar da duk wani ma’aikacin gwamnatin da aka samu…