Dokta Ahmad Abubakar Gumi ya ce akasarin malaman Musulunci da ke tara abin duniya ba su iya fada wa masu ba su kudi gaskiya, musaman gwamnati ko mabiyansu.
Ya kamata malamai su rika gudanar da rayuwa ta facaka da rungumar abin duniya ta hanyar shiga manyan motoci da sauransu?
Abin da zan ce shi ne kullum ana son mai kiran mutane zuwa ga alheri ya zama mutawassid wato mai gudun aikata abu fiye da kima. Ko ya nuna son duniya ko ya rika ci da addini ko ya zama duk wa’azin da yake yi domin samun abin duniya na. Malamai masu irin haka za su ga barna amma ba za su iya magana ba. Wannan barna ko daga hakimai ne ko gwamnati ba za su iya magana ba domin suna tsoro kada rayuwar da suka daukar wa kansu ta tsinke domin yawancin dukiyar daga wajen gwamnati ake samunta. Na biyu akwai malaman da su kuma tatse kungiya ko mabiya suke yi, wadannan za ka suna rayuwar facaka amma mabiyansu na cikin talauci da rashi. Duk dai malamin da ya dauki irin wannan rayuwa za ka ga baya iya fuskantar mutane ya yi masu wa’azi ya fada musu gaskiya gwamnati ce ko jama’a, domin idan za ka yi wa irin wadannan mutane magana sai ka guji abin hannunsu.
Sai dai duk da haka ba laifi ba ne idan malami ya samu dukiya ba ta hanyar wa’azinsa ba, ba ta hanyar karbar abin hannun mabiyansa a masallatai ba. Allah ne Ya ba shi dukiyar saboda kila manomi ne ko ya iya fatauci ko wata sana’a ya tara kudinsa babu laifi ya amfana da dukiyarsa. Domin an fi son haka saboda ko cikin Sahabban Manzon Allah (SAW) ýkamar su Usman bin Affan da Abubakar Siddik (RA) duk masu arziki ne amma wannan bai hana su zama shugabanni ba kuma ana ko yi da su.
Abin da ba a so ga malami shi ne ya dogara ga wadansu da sunan addini yana tara dukiya.
To, me za ka ce ga mutanen da sun ga malami a mota mai tsada ko gida sai a fara yi masa isgili?
Eh, to irin wannan malami a ina yake samun kudinsa, za ka ga yana da dukiya amma kuma ba ya aikin komai. ýZa ka ga yana hawa manyan motoci ko zama cikin manyan gidaje amma ba ya aiki. Don haka ina ya samu wannan kudi ita ce matsalar. Irinsu sai dai su rika fada wa gwamnati abin da suke son ji duk abin da ta yi na cutar jama’a ba za su iya yi mata tsawa ko magana ba.
Shi ya sa idan ka ga shugabannin Musulunci ko wadansu shaihunnai suna walwala da kudi irin wadanan za a iya tuhumarsu. Amma wanda hanyarsa ta samun kudi ba ta bangaren addini ba ne sai dai ma shi ya bai wa addini babu wanda zai zarge shi.
Amma duk da haka duk wani abu na nuna isa bai dace ga (ma’abucin) addini ba. Idan dukiya ce ka tsaya a tsakiya ba a son talauci ba a kuma son dukiyar da za ta cire mutum daga bautar Allah. Ai muna ganin yadda wasu biloniyoyinmu ba su da wani aiki na alheri ga su nan muna ganinsu da jirage amma babu wani aikin alheri da suke yi na taimaka wa addinin Allah. Sai biki da yawace-yawace alhalin ga mutane cikin yunwa da talauci cikin rashin lafiya.