✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malamai ku yi magana kan garkuwa da mutane – Imam Usama

Limamin masallacin Unguwar ’Yan Majalisar Dokoki ta Kasa da ke Shiyyar B, a Apo, Babban Birnin Tarayya Abuja, Imam Ibrahim Awwal (Usama) ya yi kira…

Limamin masallacin Unguwar ’Yan Majalisar Dokoki ta Kasa da ke Shiyyar B, a Apo, Babban Birnin Tarayya Abuja, Imam Ibrahim Awwal (Usama) ya yi kira ga manyan malaman addinin Musulunci na kasar nan, su fito su yi magana kan matsalar garkuwa da mutane da take faruwa a Arewa.

Imam Ibrahim Awwal ya yi wannan kira ne lokacin da yake gabatar da wa’azi a Babban Masallacin Juma’a na Unguwar ’Yan Majalisar da ke Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata.

Ya ce ya kamata manyan malaman kasar nan  irin su Sheikh Dahiru Bauchi da Sheikh Sani Yahya Jingir da Sheikh Karibullah Nasiru Kabara da Sheikh Bala Lau da sauran kungiyoyin addinin Musulunci na kasar nan su yi magana kan a daina wannan mummunan abu da ake aikatawa, na garkuwa da mutane a Arewa.

Ya ce manyan malamai da sauran masu fada-a-ji na Arewa su fito nuna wa duniya wannan abu ya isa haka don su kare mutanensu.

“Bai kamata a yi shiru da wannan abu ba, a zuba ido ana kallo. Akwai wadanda suna nan tare da jama’a a gari da suke taimaka wa wadanda suke garkuwa da mutane. Don haka ya kamata a fito a yi magana a tona asirin irin wadannan mutane,” inji shi.

Ya ce a cikin wadanda masu garkuwa da mutanen nan  suke kashewa akwai yara kanana da mata wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. Kuma yanzu ta kai ga ana tayar da yara kanana da daddare domin su yi addu’a su kai kukansu ga Allah don Ya bi musu hakkin iyayensu da masu garkuwa da mutanen suka sace ko suka kashe.

Imam Usama ya yi bayanin cewa ya kamata masu garkuwa da mutanen su ji tsoron irin wadannan addu’o’in da ake yi musu. Su kalli Allah su tuba su daina aikata wadannan miyagun abubuwa.

Sai ya yi kira ga gwamnati ta zauna da shugabannin masu garkuwa da mutanen, idan suka bayyana kansu kamar yadda aka yi da ’yan tawayen yankin Neja-Delta domin a kawo karshen wannan matsala.