✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Malamai ku guji shiga rudanin siyasa’

A lokacin da shugabanin kungiyoyin addinin Musulunci musamman na bangaren Izala ke ta bayyana ra’ayoyinsu a kan Shugaban Kasar da ya kamata a zaba a zaben…

A lokacin da shugabanin kungiyoyin addinin Musulunci musamman na bangaren Izala ke ta bayyana ra’ayoyinsu a kan Shugaban Kasar da ya kamata a zaba a zaben da ke tafe watan gobe, wani dattijo a Jihar Gombe, Malam Magaji Adamu Namusa Miringa, ya yi kira ga malaman cewa su zama masu fadakarwa a kan addini ba  ’yan siyasa ba.

Malam Magaji Adamu Miringa, ya yi wannan jan hankali ne lokacin da yake zantawa da Aminiya kan yadda shugabannin Kungiyar Izalar suka fito a kafafen watsa labarai suna bayyana ra’ayoyi masu sabani da juna kan dan takarar Shugaban Kasar da za a zaba.

Ya ce ya fi kyau malaman su fi mayar da hankali wajen koya wa mabiyansu yadda za su yi addini don a yaki jahilci a kan su rika fadi-in-fada a kafafen watsa labarai wajen nuna ra’ayoyinsu kan ’yan takara.

Dattijon ya ce ko a can baya an taba samun bambancin ra’ayoyi a tsakanin malaman Izalar, sai ga shi yanzu ma an sake samun hakan k tsakanin Shugaban Kungiyar Izala ta Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau inda ya ce a zabi Buhari shi kuwa Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum, ya ce Atiku Abubakar ne ya fi cancanta inda ya ce hakan duk bai kamace su ba.

Malam Magaji Miringa, ya ce duk da suna da ’yancin yin zabe a matsayinsu na ’yan kasa, amma bai kamata su rika nuna wa duniya cewa kansu ba a hade yake ba.

Daga nan sai ya ce a shekarar 2000 yana daya daga cikin wadanda suka je har hedkwatar Izala ta Kasa suka ba da shawarar cewa a zauna a warware matsalar da ta faru a lokacin a tsakanin ’ya’yan kungiyar don haka bai kamata a ce yanzu an sake samun matsala ba don za ta iya jawo rudani a tsakanin mabiya kungiyar ta Izala.