✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malamai 9,246 sun fadi jarrabawar koyarwa

Kimanin mutum 9,246 da suka zana jarrabawar zama malamai a watan Yuli ne suka gaza kai bantensu. A sakamakon da Hukumar Yi wa Malamai Rajista…

Kimanin mutum 9,246 da suka zana jarrabawar zama malamai a watan Yuli ne suka gaza kai bantensu.

A sakamakon da Hukumar Yi wa Malamai Rajista ta Kasa (TRCN) ta fitar, mutum 28,094 wanda ya kai kaso 75 cikin 100 ne ya suka samu nasara.

Shugaban hukumar, Mista Josiah Olusegun ya ce, “Kimanin mutum 44,363 ne suka yi rijistar jarabawar yayin da 37,340 suka rubuta ta. Sakamakon cutar COVID-19 ne ya sa mutane masu yawa ba za su iya rubutawa ba kamar yadda aka saba yi a baya”.

Mista Josiah ya kuma yaba wa kokarin da masu rubuta jarrabawar suka yi, yana mai cewa an kirkiro jarrabawar ce domin a tabbatar da kwarewa a fannin koyarwa a Najeriya.

Ya ce, “An yi kokari a ciki gaskiya. Kaso 75.24 cikin 100 sun samu nasara. Sannu a hankali malamai na kara samun kwarewa wajen amfani da na’urar kwamfuta.

“A lokacin da mu ka fara shirya jarrabawar akan samu faduwa sosai ba kamar yanzu ba.

“Makasudin fito da jarrabawar shi ne tsaftace harkar koyarwa a kasa ta hanyar tabbatar da cewa mutane ba a shigowa harkar sakaka ba tare da tantancewa ba”, inji shugaban.

Jihar Legas dai ita ce a kan gaba wajen yawan wadanda suka rubuta jarrabawar da mutane 3,574 sai kuma jihar Ekiti da ke da adadi mafi karanci na 235.

A farkon watan Nuwamba mai zuwa ne dai rukuni na gaba za su rubuta tasu jarrabawar.