✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malama Hafsat tare da mijinta Jibrin Musa Namadi da ‘ya’yansu.

Jaridar Dalilin taronsu, ta ranar kofar hanci da zagaye ga watan Yawon-wuni na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya,…

Jaridar Dalilin taronsu, ta ranar kofar hanci da zagaye ga watan Yawon-wuni na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya, ta fara bankado jimurdar waskiyar kwance-tushen kasar Haurobiya. Tunda a halin da akee ciki, ta bayyana karara cewa akwai kullalliyar rinjayar da kundin waskiyar kwance-tushen kasar Haurobiya a kan kundin batu na ingarman karfe na shekara ta alif da manuniyar kasa da ta kasa da ta kasa da ta kasa, wanda ake aiki da shi wajen tafiyar da harkokin mulkin mulka’u, sai mu tabbatar da cewa Mai Kuntigin karya lagon dokoki da Mataimakinsa, Balan-jajin Aikin yayime-yayime, sun yi amai sun lashe.
Haurobiyawa dai na da masaniya kan turka-turkar da aka sha tafkawa wajen taron tarwatsa kasa da Shugaba Mai Gudunloko don Jonatantin-mulki ya sanya aka gudanar, inda wakilan zabi tika suka cika da mamaki ganin a ranar sili da sili ga watan Yawon-wulli kan yadda aka raba musu kundin “Waskiyar kwance-tushe,” wanda aka ce musu za a kada kuri’ar raba kan masu muhawara, on a tabbatar kundin waskiya ya zama daftarin mulkin mulaka’u a Haurobiya. Da aka falle shafukan wannan kundin waskiya, sai aka fasko cewa, yana kunshe da batutuwan da suka hada da kirkiro jihohi sili da madambaci, sannan za a share kananan hukumomi kwanciyar magirbi da kwanciyar magirbi da tsayuwa isa kafa daya. Uwa-uba, bayan an raba wa wakilai wannan kundi na waskiya da yunkurin zarce fanfalakin sa-in-sa, sai aka bayar da yini sili ga kowane wakili ya je ya falle shafukan kundin, ya dawo a ci gaba da tafka mahawara. To kunji!
Wakilan Arewacin Haurobiya sun fasko cewa su ake nyfin yi wa wa ka ci, ka ta shi, ta yadda ko sun ki, ko sun so, sai an dakile su. Sannan akwai shirin ko sun turje, sai a fasa kowa ya rasa. Irin wadannan manufofi dai tuni jiga-jigan al’umma suka bayyana aukuwarsu, tun muna ji tamkar wargi, yau ga shi ta tabbata.
Cikin nufin Mai-duka, sai Ya albarkacin Haurobiya da mutane irin su Yayan-dudu, wanda ya ci Farfesun ilimi a fannin lauye-lauen dokoki. Kuma a halin yanzu ya jajirce kan cewa ba a taba bijiro musu da shirin yin watsattsaken sabon daftarin kundin waskiyar kwance-tushe ba, don haka daga ina wannan kundin ya bullo? Farfesa Yayan-dudu ya yi watsatsaken bankadaddiyar wasika ga cincirindon wakilan taron tarwatsa kasa, inda ya yi musu nuni da cewa ba su da karfin ikon kattaba wa kasar nan wani kundi na mulkin mulaka’u, amma abin takaici, shi ne, wadda ta raba wa wakilan wannan kundi, ita ce, saka-ki-tare ta taron tarwatsa kasa. Hakika farfesa Yayan-dudu namijin maza ne, domin yayi tonon silili ga masu karyar kare ra’ayin Haurobiyawa, alhalin lalitarsu kawai suka ce cikawa. Kai akwai ma wani wakilin da ya bukaci a gano musu shugabannin taron tarwatsa kasa, domin a tantance kan ko suna cikin koshin uwar jiki, kuma ’yar bola ta damke su. Muna nan muna jiran Kuntigin doke dokokin ingarman karfe, don tabbatar da waskiyar kwance-tushe da mataimakinsa mai yayime-yayimen, yayime tanade-tanaden ingarman karfen karafa, ya tabbatar waskiyar da aka cika musu lalita don su aiwatar.
’Yan makaranta kada ku ce na fara banbadanci, kuma ko furta haka, dole sai na yabi mai Sarautar sara-da-dawainiyar al’umma na birnin Dikko, domin batutuwan da ya bijiro da su a wajen taron masu kwakwazo a kafafen yada batutuwan duniya, da suka hada da akwatunan Magana, mai hoto da mara hoto da mujallu da makalu da jaridu, inda ya nuna kin karbuwar Kundin Waskiyar kwance-tushen Haurobiya. Sannan wannan gwarzon gwarza a cikin al’ummar Haurobiya, ya fasko jirgin masu kulla makircin tazrcen gudun-loko da jona-tantin mulki a karo na kofar hanci. To manyan Arewatawa, ya kamata a motsa, a motsa, a kuma jajirce, inma ta kama a fandare wa miyagun da ke shirin tarwatsa Hauriobiya don cimma soye-soyen zukatansu.
Matukar ana son cimma nasara, sai an daina yaren nasara, an zo an yi faskaren ma’anoni a cikin yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare sa-in-sa ba. Don haka nike kira ga Farfesa Yayan-dudu, duk wata kulalliya da suka tsuwurwurta, ka tabbatar ka yi faskarenta, ta yadda za mu gano asalinta da amfaninta, ko aka sin haka. Kuma ba za mu taba amincewa da duk wani kundin waskiya ba. Idan kuwa so ake yi mu rungeme shi hannu karamin lauje, to wajibi ne ya tanadi sassa daban-daban, wadanda za su bijiro da dabarun kare Haurobiyawa daga Haramta Bobo da kwambon bokoko; da ceto yaran Cibin-boko; uwa-uba a samar da manhajar koyon watsattsake mara hajijiya, ta yadda za a lalubo bakin zare a yi wa tufkar hancin hana tsallen badake da barkonon dakatar da kwadagon masu neman kadago. Idan aka bi wannan manufa, to zan shige gaba gadi wajen yi wa kowane irin kuni lakabin wagegen littafin dokokin ingarman karfen karafa, mai kunshe da manufofin warware tsilli-tsillin cukudi-cukudin da suka cukurkude Haurobiyawa.
Hakika mun ga wallen wakilan zabi tika. Kuma ya rage rowan Tumbin-wulli da Dauda-Mai-maki da gungun wkailan rafkiya da tsofaffin Haurobiya su tabuka abin a zo, a gani, wajen hana kundin waskiya bayar da damar tazarce ga masu fafutikar kankame mukamai da madafun iko, alhalin ba a bar jama’a sun kada musu kuri’in zabi-sonka ba. wannan kuwa za ta sabu, wai bindiga a ruwa?