✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malam M. B. Umar: Tunawa da marubuci, malamin Adabin Hausa

Allah Mai Girma. Tabbas! “Dukkan rai sai ya dandani mutuwa.” A ranar Laraba (7-7-2004) ce Allah Ya yi wa Malam Muhammad Balarabe Umar rasuwa, bayan…

Allah Mai Girma. Tabbas! “Dukkan rai sai ya dandani mutuwa.” A ranar Laraba (7-7-2004) ce Allah Ya yi wa Malam Muhammad Balarabe Umar rasuwa, bayan ya yi doguwar jinya. Kwanci-tashi, wannan watan ne yake cika shekaru goma da rasuwa. Wane ne M. B. Umar?
A daidai lokaci da nake kokarin amsa wannan tambaya da ma wasu, gwargwadon iko, zan yi amfani da wannan dama wajen sake yi wa daukacin ’yan uwa da abokansa da dalibai da malamai da manazarta da masana harshen Hausa, a ciki da wajen kasar nan gaisuwar ta’aziyya da masu iya magana suka ce ba ta ruba.
Marigayin tsohon malamin makaranta ne, fasihi kuma haziki a fagen Ilimin Harshen Hausa. An haife shi a ranar 23-12-1949. Ya yi karatun allo a farkon kuruciyarsa, daga baya ya shiga Makarantar Yaki Da Jahilci ta Fada, Zariya. Bayan nan ya shiga makarantar firamare ta kofar Gayan a 1961. Daga nan kuma ya shiga Kwaleji Horon Malamai Ta Sakkwato, inda ya sami Shaidar Malanta Mai Daraja Ta Biyu a 1972.
Ya fara aikin koyarwa a makarantar firamare ta Nurul Huda, Tudun Wada, Zariya. Ya shiga Jami’ar Bayero Kano, inda ya sami digirin farko a fannin Hausa da Shaidar Ilimin Koyarwa a 1978. A Jami’ar ce kuma ya yi aikin Hidimar kasa. Ya kuma sami digiri na biyu a fannin Hausa a 1980 daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
A rayuwarsa ya yi aikin koyarwa a Makarantar Firamare ta Nurul Huda, Tudun Wada Zariya. Ya yi aiki da Hukumar Lafiya ta Jihar Kaduna a matsayin mai kula da Ma’ajiyin Hukumar (Store keeper) daga 1973 zuwa 1974. Aikin koyarwa a Jami’ar Bayero Kano. Kuma Mataimakin Jami’in Tsara Jarabawa na Tsangayar Fasaha Da Addinin Musulumci a 1979. Ya zama Sakatare a Kwamitin Tsara Manhajar Karatu a 1979 zuwa 1980. Mataimakin Shugaban Tsangayar Fasaha Da Addinin Musulumci (FAIS), a bangaren Jarabawa Da Harkokin Mulki. Mamba a Hukumar Nazarce-Nazarcen Aikin Koyarwa A tsangayar Nazarce-Nazarce Na Bai daya a 1982 zuwa 1983.
Wasu ayyukan koyarwa da ya yi a matsayin malami mai ziyara sun hada da Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, a Sashen Diploma ta Hausa na lokacin hutu (Sandwich Programme) a 1981 zuwa 1985, ya koyar ne a fannonin Adabi, Al’adu da Harshe. A Jami’ar Maiduguri, ya kasance Malami mai Ziyara a 1984 zuwa 1985. A Kwalejin Horon Malamai ta UPE Kano, 1976 zuwa 1977. A Kwalejin Horar Da Malamai ta Wudil, a 1978 zuwa 1980. Shugaban Hukumar Fasaha da Al’adu ta Jihar Kaduna (Karo na Farko). Editan Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo. Mataimakin Darekta a Hukumar Kula Da Bankunan Al’umma ta kasa (NBCB). Shugaban Shiyya na Hukumar Kula da Bankunan Al’umma ta kasa (NBCB). Shugaban Hukumar Fasaha da Al’adu ta Jihar Kaduna (Karo na Biyu). Aikin Koyarwa a Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta Zariya. Shugaban Sashen Harsuna. Ya rike Mukamin Shugaban Tsangayar Harsuna. Mamba Hukumar Gudanarwa ta Makarantar. Wakili a Hukumar Ilimi Ta Bai daya Ta kasa (UBE). Shugaban Kwamitin Gina Babban Masallacin Makarantar. Mamba a Kwamitin da’a. Shugaban Tsare-tsare na Karatun karshen Mako, duk a Kwalejin Ilimi Ta Tarayya ta Zariya.
Wasu littattafan da marigayin ya rubuta sun hada da na zube kamar, Gari Ya Waye, kadangarun Birni, Son Maso Wani, Marigayi Murtala Muhammad da Talaka: Gugar Yasa? Na wakoki sun hada da Wakoki Tara, Wakoki Don Yara, kwaryar kira, Zancen Zuci da kuma Wakokin Ta’aziyya. Na wasan kwaikwayo sun hada da kalubalen ’Yan Boko, Kama Da Wane da kuma Kowa Ya ki Ji. Sai littattafan nazarin adabi da al’adu da suka hada da dan Maray Jos Da Wakokinsa, Camfe-Camfen Hausawa, Wasannin Tashe, Sallar Gane A Daura, Adabin Baka (Don Makarantu), Nazrin Al’adun Hausawa, Nazarin Rubutattun Wakoki, Dangantakar Adabi da Al’adu (1-2), Al’adun Haihuwa A kasar Hausa, Sana’o’in Gargajiya, Wakokin Baka, Asalin Wasa Tsakanin Hausawa, Bukukuwan Gargajiya da kuma Laccoci Da Makaloli A Kan Adabi Da Al’adun Hausa. Na addini sun hada da Biyayya Ga Iyaye, Kyawawan dabi’u, Sallah Da Muhimmancinta, Muhimmancin Zakka, Fa’idojin Azumi, Aboki Nagari, Kawa Tagari da kuma Rayuwar Magabata. A fannin Ingilishi kuwa, shi ne Babban Edita kuma Mawallafin Mujallar dalibai ta Juniors Digest. Shi ne kuma Editan Effectibe Language Teaching da “ZAJOLS” (Zaria Jonals of Language Studies).
Marigayin ya rasu ya bar matan aure uku da kuma ’ya’ya 21, maza 13, mata 8. Kodayake ya haifi ’ya’ya 24 ne, uku (dukkansu mata) sun riga shi rasuwa. Marigayin, ya sauke dukkan hakkokinmu da ke wuyansa a matsayin mahaifi, kafin komawarsa ga Mahaliccinsa. Mutum ne mai kyakkyawar alaka tsakaninsa da iyalansa, mai son zumunci da kuma tausayin masu karamin karfi. Yana da barkwanci, yakan ba mu labarai masu kunshe da darassu mabambanta. Lokuta da dama yakan gabatar da batutuwa don muhawara da wasa kwakwalwa. Misali, ya taba yi mani wata tambaya kamar haka:
Ya ce, “gida biyu…” Ni kuma na ce, “maganin gobara.” Ya ce, “a’a.” Ya maimata tambayar sau uku, ni kuma ina cewa, “maganin gobara.” Sai daga karshe ya ce in ba shi gari, bayan na bayar, sai ya ce: “Gida biyu maganin kwana waje in an yi gobara.” Akwai ire-iren wadannan misalai masu dimbin yawa.
Game da halayensa Farfesa dalhatu Muhammad(ABU) ya ce: “Marigayi, ka kira shi da duk sunan da ake kiran mutanen kirki domin shi ma ya cancanci irin wannan suna saboda matukar kirkinsa” (H.T., kundin bincike, BUK, 2008).
Alhaji Adamu M. M. (Bunun Hadeja) ya ce: “Na yi farin ciki da ba ni wannan dama. Na san M. B. Umar a matsayin dalibi da kuma malami. Abokina ne, na san shi da gaskiya da rikon amana. Mutum ne mai zumunci da sanin ya kamata. Yana da jajircewa a kan  duk abin da ya saka a gaba. Mutumin mutane ne wanda kayansa bai rufe masa ido ba. Kullum muna Addu’a Allah Ya Jikansa, Ya saka masa da alkheran da ya shuka da Jannatul Firdaus.” (23-06-14).
Malama Ai’sha Wali (FCE Zariya): “Malam M. B. Umar mutum ne mai saukin kai da kuma barkwanci. Mutum ne kuma mai yawan kyauta domin abin duniya ba ya rufe masa ido. Wani abu game da shi, shi ne ya na sha’awar rubuce-rubuce da karfafawa a yi.” (H.T., kundin bincike, BUK, 2008).
Malam Tukur Isiyaku (Editan Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo): “Marigayi M. B. Umar mutum ne mai saukin kai, mai kuma Jama’a. Sannan kuma yana sha’awar rubuce-rubuce. Ta bangaren shugabanci ba ya kama-karya.” (H,T., kundin bincike, BUK, 2008).
Alhaji Abdulmumini Yakubu Ashir (Darektan Hukumar Fasaha Da Al’adu Ta Jihar Kaduna): “Marigayi mutum ne mai dauriya da kuma kwazon aiki. Saboda kwazon aikinsa ne ma, akwai lokacin da muka yi kwanaki uku da shi muna aiki a ofi. Sai dai kawai mu koma gida mu ci abinci mu yi wanka mu dawo ofis mu ci gaba da aiki.” (H.T., kundin bincike, BUK, 2008).
Burin marigayi ne, ya ga Hausa ta zama Harshen kasa a Najeriya, domin a cikin manyan harsuna guda uku da ake da su a Najeriya, Hausa ce kan gaba don ta wuce tsara.
Magana ta gaskiya, damar da na samu ta yi min kadan da zan iya bayyana ayyukan marigayi na alhairi. Shi ya sa na yi nazarin a takaice, don abin da yawa wai mutuwa ta shiga kasuwa.” Amma idan na ji jama’a na cewa malam ne ya sama mun aikin yi, ko shi ya sama mun takardar shiga makaranta, ko ya yi mun hanya na samu alherai. Idan na dubi kokarins na gina rijiyoyi a wurare daban-daban da gina masallatai, misali na jikin gidansa a Unguwar kwarbai Zariya, wanda ake kira da suna ‘Masallacin MB,’ sai in ce Allah Ka gafarta wa wannan bawa naKa, Ka ba mu ikon aikata alheri kafin kwanakinmu su kare, don dai babu wanda zai dawwama, kamar yadda Dokta Aliyu Namangi ke cewa a daya daga baitocin shahararriyar wakarsa ta Infiraji: “Sa idon natsuwa ka duba/ Duniya ba mu zo zama ba/ Dubi Hairul hakki in ba/ Wauta da rashin natso ba/ Ka tuna ba za mu dawwama ba.”
Daga karshe, a daidai lokacin da nike gabatar da nazari kan kakaitaccen tarihi, aikace-aikace da kuma kadan daga gudunmuwar M. B. Umar, kan adabi da al’adun Hausa, bayan shekaru goma da rasuwarsa, a hakika, babu abin da zan ce baya ga fatar Allah Ya yafe masa kura-kuransa, Ya yi masa sakayya da Aljannar Firdaus, amin-summa-amin.
Aminu, dalibi ne mai karatun digiri a fannin Hausa da llimin shaidar koyarwa(BA.ED) a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Najeriya (08036897982), [email protected]