✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maku ya bukaci a zakulo makasan Mashal Badeh

Tsohon Ministan Labarai kuma dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a Jam’iyyar APGA, Mista Labaran Maku ya bukaci Rundunar Sojin Najeriya da Gwamnatin Tarayya su gudanar…

Tsohon Ministan Labarai kuma dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a Jam’iyyar APGA, Mista Labaran Maku ya bukaci Rundunar Sojin Najeriya da Gwamnatin Tarayya su gudanar da cikakken bincike a kan kisan gillar da wadansu ’yan bindiga suka yi wa tsohon Hafsan Tsaro, Iya Cif Mashal Aled Badeh.

Mista Labaran Maku ya yi wannan kira ne lokacin da yake kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa a garin Karu, Jihar Nasarawa. Ya ce ya kamata yanzu a ce Rundunar Sojin Kasar nan da Gwamnatin Tarayya suna gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin kisan Aled Badeh su kuma gano makasansa don su fuskanci hukunci.

Ya ce “A gaskiya na kadu sosai da na samu labarin kisan gillar da aka yi wa tsohon Hafsan Tsaron wanda ya yi aiki a karkashina a lokacin da nake kula da harkokin Ma’aikatar Tsaro ta kasar nan. Marigayin mutum ne mai ilimi da ya san ya kamata wanda ya sadaukar da komai wajen bauta wa kasar nan a lokacin da yake raye. Saboda haka bai kamata a kyale duk wanda ke da hannu a kisansa ba. A yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar an zakulo su an kuma gurfanar da su a gaban kotu,” inji shi.

Daga nan sai dan takarar Gwamnan na APGA ya tabbatar wa dimbin magoya bayansa da suka halarci gangamin cewa idan al’ummar jihar suka zabe shi a matsayin Gwamna, abu na farko da zai bai wa fifiko shi ne fannin tsaron lafiyarsu da dukiyoyinsu. Ya kuma nuna takaicinsa game da yadda garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka suka zama ruwan-dare a jihar. Kuma ya ce a yanzu manoma ba sa iya tafiya gonakinsu don tsoron harin makiyaya da sauran mayakan kabilu a jihar da sauransu.

Ya bukaci magoya bayan jam’iyyarsa ta APGA da al’ummar jihar su fito kwansu da kwarkwata su zabi ’yan takarar jam’iyyar daga sama har kasa don ba su damar samar musu da ainihin ribar dimokuradiyya.

Idan za a iya tunawa a kwanaki ne wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka harbe Badeh a hanyarsa ta zuwa gonarsa da ke Karamar Hukumar Kokona a Jihar Nasarawa.