Kwana 37 da sallamar tsohon Ministan Noma, Sabo Nanono tare da takwaransa na Ma’aikatar Wutar Lantarki, Sale Mamman, amma har yanzu Shugaba Buhari bai maye gurbinsa da wani ba.
Tun bayan cire ministocin a ranar 1 ga watan Satumba, manyan ’yan siyasa daga jihojin Kano da Taraba, inda Nanono Sale Mamman suka fito ke ta kira da a maye gurbin Nanono da wani dan asalin jihohin.
- Saukin yin kasuwanci: Yadda Gombe ta yi zarra tsakanin jihohin Najeriya
- Buhari ya sallami ministan noma da na lantarki
Sun ce a jahohin ya kamata a sake zaben wasu ministocin domin maye gurbin wadanda aka sallama, duba da yadda a halin yanzu jihar Kanon minista daya kawai take da shi, ita kuwa Taraba ko guda ba ta da shi.
Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kuma jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Sulaiman Abdulra’uf, wanda a ka fi sani da Kawu Sumaila, ne ya yi kiran yana mai roko da a mai da mukamin ministan noma zuwa jihar.
Kawun, ya kara da cewa akwai mutane da suka cancanta a basun mukamin a jihar, har ya ba da misali da irin su Ismael Buba Ahmad.
Hakazalika, Honorabul Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda wanda shi ma jigo ne na jamiyyar a Kano, ya roki Shugaba Buharin da ya taimaka ya zabo sabon ministan noma daga jihar.
Shi ma Shugaban Matasa JIhar Kano na Jamiyyar APC, Alhaji Sule Shuwaki kira yayi da gwamnati ta gaggauta maye gurbin da wasu ’yan asalin jahar.
A jihar Taraba ma Aminiya ta gano cewa yan siyasa na jihar sun nuna rashin jin dadin su da yadda har zuwa wannan lokaci ba a nda sabon ministan ba.
Kuma akalla mutum 32 ne ke neman maye gurbin tsohon minista Sale Mamman.
Daga Ibrahim Musa Giginyu, Kano da Magaji lsa Hunkuyi, Jalingo da Muideen Olaniyi da Abudallahi Umar Abubakar