✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makirci ne ya durkusar  da masakun Arewa  – Musa Bala

Aminiya ta zanta da wani tsohon ma’aikacin masaka Alhaji Musa Bala Aliyu wanda ya kwashe shekara 42 yana aikin kafin ya yi ritaya a shekarar…

Aminiya ta zanta da wani tsohon ma’aikacin masaka Alhaji Musa Bala Aliyu wanda ya kwashe shekara 42 yana aikin kafin ya yi ritaya a shekarar 2007, inda ya bayyana yadda makircin Yarbawa ya yi tasiri har masakun da ke Arewa suka durkushe:

 

Shekara nawa ka yi kana aiki a masaka?

Na yi shekara 42 ina aiki a masaka. Na fara aiki a 1965 kuma na aje aiki a shekarar 2005, sai kuma shugabannin ma’aikatan suka matsa mini cewa in ci gaba da aiki da su a matsayin kwantaragi, saboda haka na kara shekara biyu sai na ce su bar ni in huta, don haka na bar aiki gaba daya  a shekarar 2007, ka ga shekara 42 ke nan.

A wace masaka ka yi aiki kuma da wani matsayi ka fara?

Na yi aiki ne masakar da ake kira United Nigeria Tedile Limited (UNTL), kuma na fara ne daga karamin ma’aikaci. Daga baya sai aka tura ni koyon aikin hada sinadaren yin rini a birnin Manchester da ke Ingila. Kuma na je kasar Swaziland daga baya na dawo wani gari da ake kira Pataland a kasar Jamus. Bayan da na dawo sai aka ba ni mukamin mai kula da ma’aikata. Daga nan kuma na sake samun tallafin karo ilimi daga Majalisae Dinkin Duniya zuwa kasar Poland a 1974.

Bayan da na dawo sai na koma bakin aiki a matsayina na mai kula da ma’aikata da ke hada sinadaran rini da kuma na’urorin da ke sarrafa sinadaran rinin. Sai kuma a 1976 aka sake tura ni birnin Chelsea a Ingila. To sai dai wannan tafiyar ta sha bamban da sauran domin na yi ta ce a kan tace ruwan da masaka take amfani da shi, bayan na dawo kuma sai aka sake tura ni Scortland na kara koyo yadda ake tsabtace ruwa. Bayan na dawo sai kamfanin UNTL ya sayi masakar Nospin a 1984, aka sa mata suna Super Tedt, sai aka tura ni a matsayin manaja, har na kai babban manaja.

Yaya kuka rika aiki a masakar?

Aikace-aikacen da masakar ke yi suna da yawa. Da farko masakar tana rini ne kawai, muna sayo zani  sakakke daga wata masaka sai  mu yi rini, mu wanke mu yi zane ko rubutu, sannan mu sayar.

Daga ina kuke sayowa?

Muna saye a nan gida Najeriya wasu kuma daga kasar waje. To daga nan sai gwamnati ta fito da wani tsari na cewa (Backward Integration) a faro aiki daga tushe. A lokacin sai muka bude wajen yin zane da kanmu, inda muka bude sassa biyu da suka kunshi aikin saka baki daya da sashin saka zare ko murza zare da saka na zanen da za mu yi aiki. Sai ya zama mu za mu yi zare, mu saka zane, mu wanke mu yi rini sannan mu yi zane ko rubutu, sannan mu wanke mu sayar ga jama’a.

Masaku nawa ne ake da su a garin Kaduna a lokacin?

Muna da masaku a garin Kaduna guda bakwai. Akwai wanda aka fara kafawa ita ce Kaduna Tedtile Limited (KTL) sai United Nigerian Tedtile Ltd (UNTL) da Super Tedt da Nospin da Arewa Tedtile  sai Notedt da Northern Tedtile sai kuma masakar da ake saka gwado.

Akwai masakar da take karkashin gwamnati, ko duka na ’yan kasuwa ne?

Eh akwai na gwamnati ita ce KTL wadda marigayi Ahmadu Bello Firimiyar Arewa  ya kafa. Sai Notedt ita kuma ta gwamnatocin Arewa ne sai Arewa Tedtile wadda hadin gwiwa ne da mutanen kasar Japan, amma UNTL ta mutanen kasar Sin ce.

Ko za ka iya fada mana yawan ma’aikatan masaku kafin su durkushe?

Ba zan iya cewa gaba daya na sani ba, amma na san a masakun da suke karkashin UNTL za a samu ma’aikata sama da dubu 12 . Idan ka hada masakun da ke garin Kaduna akalla ma’aikata su kai dubu 30.

Ina da ina  kuke kai kayayyakin?

Atamfofin da muke yi ’yan kasuwa na dauka har zuwa kasar Amurka da kasashen Afirka baki daya. Saboda kyau da tsari na zannuwanmu, kasar Ghana ta nemi mu bude reshe a kasarta kuma Kamfanin UNTL ya bude masaka  mai suna  Akasumbo Tedtile, kuma atamfofin da ake sakawa a kasashen duniya ba wanda ke ja da mu sai ta kasar Holand.

Ta yaya kuke samun audugar da kuke amfani?

A gida Najeriya muke samun mafi yawan audugar da muke amfani. Ka ga lokacin da masaku ke aiki, ni din nan an taba tura ni Adamawa domin karfafa gwiwar manoma don su noma auduga, tare da raba musu irin auduga da maganin feshi da taki. Sannan idan suka noma audugar kuma mu saya a kan farashin da ake sayarwa

Mafi yawan kayan aiki da muke raba wa manoma kyauta muke ba su saboda a jawo hankalinsu. Ka ga a nan ma ana amfana kwarai da gaske.

Kamar wasu jihohi ne suka fi noma auduga a Arewa?

Ai kusan duk jihohin Arewa babu inda ba a noma auduga sai dai akwai wadanda suka fi. Akwai jihohin Taraba da Gombe da Bauchi da Borno, kuma akwai Jihar Neja da Kwara sannan uwa uba Jihar Katsina. Domin noma auduga da suke yi Kamfanin UNTL ya kafa masaka da ake kira Funtua Tedile da tsohowar Jihar Sakkwato nan ma muna da masaka mai suna Zamfara Tedtile.

To ita audugar me da me ake amfana a jikinta?

Madallah, ka fara zuwa inda nake so mu kai. To na daya shi ne fatar audugar za a mayar da ita zare a saka zane da ita, shi kuma irin ya koma wajen manoma domin su sake shukawa, sauran mu sayar wa kamfanonin da suke tatsar man girki daga cikin guryar sannan a samu kuli-kuli a jikin man da aka tatsa. Ka ga ya zama tunkuza to wannan shi kuma ya zama abincin dabbobi, ita kanta guryar Fulani suna sayen don su ba shanu.

Yaya za ka kwatanta asarar da mutuwar masakun ta jawo wa al’ummar Arewa?

A gaskiya kokarin tabbatar da ajanda ko in ce kudirin Yarbawa da suke da shi na kashe dukan masakun da ke Arewa gaba daya ce. Kuma duk fitinar da muke ciki wannan ajanda tana cikin abubuwan da suka kawo mana. Su ne suka kawo mana dukan fitinar da muke ciki, amma Allah ne Ya san gaibu. Ina da dalilai wadanda zan bayar cewa sakacin ko kuma da wata manufa na gwamnati ne suka hallaka wadannan masaku domin abubuwan da suka kashe masaku ba wai jari ba ne ba su da shi, kuma ba wai ba kayan aiki ba ne ko ba kudi, an saka su cikin wani matsayin da ba yadda za a yi su ci gaba.

A maganar asarar da mutuwar masaku ta jawo wa wannan kasar, musamman Arewa ba ta musaltuwa. Domin ita kanta gwamnati kudin da take samu na haraji ko shi kadai zai iya rike ta domin miliyoyin kudin da take samu. Sannan ka ga kudin da ake biyan wutar lantarki shi ma kawai ba kadan ba ne. Mu muke jawo ruwan da muke amfani da shi da kanmu amma abin da muke biyan haraji a duk wata na gidan ruwa shi ma ba kadan ba ne. Kuma mutanen da suke kusa da masakun suna amfana da asibitin  masakun ne kuma idan ka zo bakin masaka za ka ga yadda ake kaiwa da komowa kai ka ce ita ce babbar kasuwar Kaduna, baya ga ma’aikata da masu saye da sayar da kayan masaku, amma yanzu duk ba wadannan. Saboda haka tun daga jagororin kamfanin da ma’aikansa da manoma auduga kai har da makiyaya duk kusan asarar kulle masaku ta shafe su.

Kamar yadda ka dade kana aikin masaka, da gwamnati za ta nemi a ba ta shawarar yadda za a dawo da masaku me za ka fada?

Ba wani abu ba ne mai wahala koda yake yanzu rabona da masaka ya kai shekara 11, yanzu ba ni da wani abu da zan iya ba da labari amma dai a sanina tun a wancan lokaci da masaku suka durkushe ba wai kudi suke ne ba, wasu abubuwa ne suka rasa kamar su wutar lantarki da ruwa da kuma man da suke aiki da shi. Da suna samunsa kai-tsaye daga tushen da ya kamata to da har yanzu masakun suna nan a raye. Amma kamar yadda na fada cewa ajanda ce ta durkusar da su sai ya zama ta wadannan abubuwan na kashe lantarki da hana man da za su yi aiki da shi da barin boda a bude a rika kawo kayan da ba su da ingancin namu ana sayarwa a kan farashi mai sauki duk suka kawo mana durkushewa. Har sai da muka zama matattarar duk wani kayan da aka dauko daga kasashen waje.

Amma tunda wannan gwamnati ta fara tunanin dawo da harkar noma, in Allah Ya yarda ta fara shawo matsalolin ’yan Arewa. Ta kuma kulle boda don kada a shigo da kayan abinci daga waje ga kuma kokarin da take yi na samar da wutar lantarki da kuma samar da hanyuyin jiragen kasa da  titunan mota, to muna sa ran nan ba da dadewa ba za mu dawo cikin hayyacimmu, in Allah Ya so. Kuma masakun za su tashi. Yin hakan zai kara kawo raguwar tashe-tashen hankalin da ake fama da su.