A ranar Alhamis 29 ga watan Oktoba ne Musulman duniya suke bikin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi inda jihar Gombe tabi sahun sauran kasashen musulmi dan tuna wannan rana.
A jihar Gombe da ke Arewacin Najeriya, makarantun Islamiyya fiye da dubu hudu ne suka fito don wannan zagayen inji shugaban Kungiyar Makarantun Islamiya na jihar, Alhaji Muhammad Nuhu.
Alhaji Muhammad Nuhu ya kuma bayyana hakan ne a lokacin da yake zanta wa da Aminiya inda bikin Maulidin na bana ya yi armashi duk da kalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan kasar.
Muhammad Nuhu, ya ce jami’an tsaro sun taka rawar gani wajen basu kariya don ganin bikin maulidin ya gudana cikin nutsuwa ba tare da tashin hankali ba.
Ya ce makarantu daga fadin jihar wasu daga makwabta ta gabar yankin jihar Borno da suka fi kusanci da Gombe irin Kwaya Kusar da Bayo da sauran yankunan da ke Yammacin jihar Borno, duk sun shigo jihar Gombe don wannan zagayen bikin na maulidi.
A cewar Malaman Makarantun Islamiyya da kuma shugabannin shirya wannan taron sun taka rawar gani sosai da jami’an tsaron sai kai da Yan agaji da sauran su.
Wasu daga cikin Malaman makarantun Islamiyya da suka zanta da Aminiya sun yabawa tsarin da aka bi a wannan shekarar domin a cewar su shugabannin kwamitin shirya maulidin sun yi kokari domin tsarin da suka fitar ya yi dai dai kuma sun bi.