Mkarantar Tazkiyya da ke Unguwar Mil 12 a Legas ta yi bikin yaye dalibanta karo na biyu inda ta yaye dalibai maza da mata 19 ciki har marayu 9.
Alhaji Dauda Tarai daya daga cikin iyayen makarantar ya shaida wa Aminiya cewa akwai yaran da iyayensu maza suka rasu suka bar su wadanda iyayensu mata ba sa iya daukar nauyinsu, sai kwamitin makarantar ya dauki nauyin karatu da dawainiyarsu a abin da ya shafi kudin makaranta da abincinsu da lafiyarsu, “Yanzu haka akwai dalibai marayu 70 a wannan makaranta wacce aka kafa ta shekara 7 da suka shude inda a baya ta yaye dalibai 17 da suka yi saukar karatun Alkur’ani Mai girma, a bana kuma dalibai 19 ta yaye,” inji shi.
Alhaji Haruna Muhammad Shugaban Kasuwar Mil 12 yana daya daga cikin shugabannin makarantar ta Tazkiya, a nasa jawabin, kira ya yi ga daliban da su yi amfani da ilimi da tarbiyyar da aka ba su a lokacin karatunsu a makarantar, kuma su yi kokarin koya wa na baya. Ya ce amfanin ilimi shi ne aiki da shi kuma mafi alherin mutane shi ne wanda ya koyi ilimi sannan ya koyar da shi, “Ina kira ga iyaye su ba da himma a karatun ’ya’yansu domin babu abin da za a bar wa ’ya’ya da ya wuce ilimi da tarbiyya,” inji shi.
Kazalika ya yaba wa jama’ar da suke tallafa wa marayun makarantar da daukacin malaman makarantar.