Makarantar Islamiyya ta kungiyar Musulmi maza da mata (Association of Group of Muslim Brothers And Sisters -AGOMBAS) da ke a titin Malumfashi a unguwar Tudun Nufawa, Kaduna ta yi bikin saukar Alkur’ani, inda ta yaye dalibai 43 maza da mata.
Da yake tattaunawa da Aminiya a wajen saukar, Shugaban Sashen Kudi na makarantar kuma malamin addinin Musulunci, Ustaz Mustapha Abdulraheem, jan hankalin iyaye ya yi wajen ilmantar da ’ya’yansu.
Ya ce babu wani abu ko gado da mahaifi zai bar wa dansa ko ’yarsa kamar ilimin zamani da na addinin Musulunci, don haka ya roki su daure su tabbatar da yaransu sun yi karatu. “Babu wata kyauta ko gado da iyaye za su yi wa ’ya’yansu kamar ba su ilimin addinin Musulunci da na zamani. Kai, dole ne uba ya tabbatar ya ilmantar da dansa ko ’ya’yansa. Idan kuwa ya ki a ranar alkiyama, sai yaran sun kalubalanci iyayensu a kan kin ilmantar da su,” inji shi.
A cewarsa, an kafa makarantar ne kimanin shekaru talatin da suka wuce. Ya kuma mika godiyarsu a kan yadda aka yi bikin saukar Alkur’anin cikin sauki da nasara.
dalibai masu sauka sun karanto ayoyin Alkur’ani, daga bisani aka yi musu tambayoyi a kan nahawu, sannan aka mika musu shahadarsu da kuma Alkur’anai a matsayin kyaututtuka.
Makarantar Islamiyyar kungiyar AGOMBAS ta yaye dalibai 43
Makarantar Islamiyya ta kungiyar Musulmi maza da mata (Association of Group of Muslim Brothers And Sisters -AGOMBAS) da ke a titin Malumfashi a unguwar Tudun…