Makarantar Horar da Limamai da Ladanai da Alkalan Musabakar Alkura’ni Mai girma ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta Kasa da ke garin Jos a Jihar Filato, ta yaye dalibai 2002 daga lokacin da aka bude ta a shekarar 2001 zuwa bana. Shugaban makarantar Hafiz Aminu Yusuf Nuhu ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi a wajen yaye daliban makarantar na bana da aka gudanar a garin Jos, inda ce a bana sun samu sababbbin dalibai 233 daga jihohi 22 na Najeriya da Jamhuriyyar Nijar.
Ya ce Shugaban Kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ne ya kafa makarantar a shekarar 2001 domin amfanar da al’ummar Musulmi, wajen samar da kwararrun alkalan gasar Musabaka da kwararrun limamai da ladanai a al’ummar Musulmi.
Ya ce kungiyar ce kadai a Najeriya ta kafa irin wannan makaranta. Don haka ya yi addu’ar fatan alheri, ga wanda ya kafa makarantar.
Ya yi kira ga daliban da aka yaye su koma garuruwansu, su shiga birane da kauyuka su yada abubuwan da aka horar da su, domin amfanin al’ummar Musulmi baki daya.
Da yake jawabi a wajen yaye daliban, Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa ta Kungiyar JIBWIS, Sheikh Sani Yahya Jingir ya ce duk wanda ya ki karatu ya bar hanyar alheri.
Ya ce wadannan dalibai da makarantar ta yaye, kamar an karantar da duniya ce, domin kowannensu zai je ya yada ilimin da aka karantar da shi.
Sannan ya yi kira ga daliban da aka yaye su je su karantar da addinin Musulunci kamar yadda aka karantar da su. Kuma su rike gaskiya, domin duk wanda ya samu nasara dole sai da ya rike gaskiya.