✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Aminil Islam ta yaye dalibai 14

A ranar Lahadin da ta gabata ce Makarantar Islamiyya ta Madarasatu Aminil Islam da ke Hayin Banki a Kaduna ta gudanar da taron walimar saukar…

A ranar Lahadin da ta gabata ce Makarantar Islamiyya ta Madarasatu Aminil Islam da ke Hayin Banki a Kaduna ta gudanar da taron walimar saukar karatu, inda ta yaye dalibai 14.

Da yake jawabi a wajen taron, Sarkin Hayin Banki Malam Mahmud Shehu Galadima ya sanya wa daliban makarantar albarka, sannan ya hore su da ci gaba da neman ilimi tare da yin aikin da abin da suka koya. Sannan ya yi wa daliban da makarantar baki daya fatan alheri da murnar wannan walima da suka yi.

Da yake zantawa da wakilin Aminiya, shugaban makarantar, Injiniya Bello Yunus ya ce ya  ji dadi da farin cikin ganin wannan rana da ake yin walimar saukar karatun Kur’ani na makarantar, “Ka san wannan ne karo na farko da nake jagorantar sauka a makarantar, saboda asalin shugaban Allah Ya karbi ransa bayan ’yan ta’adda sun kashe shi kusan shekara daya da ta wuce Ina masa addu’ar Allah Ya sa ya huta, kuma Allah Ya kai hasken da ladar karatun nan kabarinsa.”

Bello Yunus ya ce, “Wannan makaranta ce mai tarihi. Marigayi Sheikh Yusuf wanda wana ne, ya yi gwagwarmaya wajen duk ayyukan addini. Amma kuma abin takaici yadda wadansu suka kashe shi da tare da laifin komai ba. Amma abin farin cikin shi ne yadda ya rayu kuma ya rasu a harkar addini.

“Marigayi Sheikh Yusuf ya fara kafa makarantar nan ne da nufin koyar da dalibai musamman matasa, babu wanda ya taba tunanin makarantar za ta kai haka. Amma da yake ya fara abin da ikhlasi, sai ga shi makarantar ta kai inda ba mu yi tunani ba. Marigayi mutum ne mai son yada addinin Allah. Yakan shiga kauyuka yana wa’azi, sannan yakan zagaya cikin gari, musamman bangaren Kiristoci yana yi musu wa’azi tare da mukabala da harshen Ingilishi. Ya sha wahala sosai a harkar da’awa, amma muna godiya ga Allah bisa irin rayuwar da ya yi, kuma ya rasu a kanta,” inji shi.

An gudanar da walimar ce a Masallacin Sultan Bello inda daliban makarantar da masu saukar suka yi karatun Alkur’ani da sauran darussa, kuma Abdullahi Mustafa ya zama gwarzon dalibai a bana.