✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makaranta ta yaye dalibai a karon farko

Makarantar Shaikh Abubakar Gumi da ke barikin Kwastam a Unguwar Amokoko da ke daura da Alaba Rago ta yi walimar saukar karatun dalibai 15 a…

Makarantar Shaikh Abubakar Gumi da ke barikin Kwastam a Unguwar Amokoko da ke daura da Alaba Rago ta yi walimar saukar karatun dalibai 15 a karo na farko a tarihin kafuwar makarantar shekaru tara da suka shude.

Shugaban makarantar, Malam Abdallah Saleh ya shaidawa Aminiya cewa makarantar ta shirya walimar saukar karatun Alkur’ani mai girma ne a karshen makon da ya gabata domin farin cikin matakin da makarantar ta taka tun bayan kafuwar ta, ya ce an kafa makarantar  ce da Iyalai uku, inda aka fara da dalibai 5 ake kuma yin karatun a gidan daya daga cikin shugabanin yankin a barikin na kwastam, kafin daga bisani makarantar ta yadu har ta kai ga an gina masallaci, wadda kawo yanzu a cikin masallacin ake gudanar da al’amuran makarantar.

Ya ce “mun sanya wa makarantar sunan Marigayi  Sheikh Abubakar Gumi ne, kasancewarsa daya daga cikin wadanda suka bada gudunmawa wajen yada addinin musulumci a yankin, tun daga wannan lokaci a cikin  masallaci muke koyawa yaran wannan yankin karatun addini da tarbiyya, don haka ne muka yi amfani da wannan lokaci na walimar saukar karatun yaran, inda muka kaddamar da gidauniya domin neman taimakon samar da fili da ginin makaranta wanda zai zamo bigiren makarantar na dindindin,”

“Don haka muke mika kokon bararmu ga duk mai iko da ya shigo ya taimaka wajen samarwa ‘ya’yan musulmin wannan yankin wurin da za a ci gaba da koyar da su addini da tarbiyya baki daya, ‘yanzu haka akwai wani kango mai daki 11 da muke sa ran mallakarsa wanda in Allah Ya taimakemu muka kai ga samun kudin sa naira miliyan 10 zamu gyara shi mu mayar da shi cibiyar koyon karatun addinin musulumci da ma ilimin zamani, domin zamu fadada sha’anin koyo da koyarwa, da zarar mun cimma nasarar mallakar wajen domin a yanzu a masallacin da muke koyarwa a ciki akwai yawan cunkoson dalibai wanda yake kawo mana cikas a yayin karantarwar,” inji shi.

Dalibai mata 11 da maza 4 ne suka yi saukar karatun Alkur’ani Mai Girma a makarantar ta Abubakar Gumi wadanda suke cike da farin ciki da jin dadi a lokacin walimar saukar karatun nasu.