✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makaman Yaki na Kirista (7)

Mu yi wa Allah Madaukakin Sarki godiya saboda ya sa muna cikin masu rai a yau ba domin komai ba sai dai alherinSa kawai zuwa…

Mu yi wa Allah Madaukakin Sarki godiya saboda ya sa muna cikin masu rai a yau ba domin komai ba sai dai alherinSa kawai zuwa gare mu. Kamar yadda muka yi magana a koyarwar da muka yi makoni da suka gabata, cewa wannan yaki ba na nama da jini ba ne ko kadan, amma na Ruhu ne, idan kuwa yakin Ruhu ne; babu wanda zai iya cin nasara da makamai na jiki kawai; dole ne mu nemi makamai masu inganci na Ruhu wadanda za mu iya yin amfani da su domin mu ci nasara bisa Shaidan da sauran ma’aikatansa. Wannan irin yaki ya fi irin yakin da ake yi a wannan duniya. Maganar Allah na cewa, ku yafa makamai na Allah, domin ku samu ikon da za ku yi tsayayya da dabarun Shaidan, ashe wadannan makamai na Allah ne, kuma za mu yi wannan tsayayya da dabarun Shaidan ne, Shaidan yana da dabaru da yawa, rashin gane wadannan dabarun Shaidan ne yakan kawo kasawa cikin yawancin abin da mu ke yi. Ina so mu ga wadannan makamai da kuma yadda suke aiki a cikin rayuwarmu ta yau da kullum a cikin wannan duniya;  mu sake komawa cikin Littafin Afisawa 6 : 14 – 17; maganar Allah tana cewa, “Ku tsaya fa, ku daure gindinku da gaskiya, kun yafa sulke na adalci, kun daura wa sawayenku shirin bishara ta salama, musamman kuma, ku dauki garkuwa ta ban-gaskiya, wadda za ku iya bice dukkan jefe-jefe masu wuta na mugun da ita, ku dauki kwalkwali na ceto kuma da takwabin Ruhu wato maganar Allah.” Idan muka duba bayanin wannan a cikin sabon Hausa kuwa ga yadda za mu karanta wurin, “Saboda haka fa ku dage, Gaskiya ta zama damararku, Adalci ya zama sulkenku, shirin kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a kafafunku. Ban da wannan kuma, ku dauki garkuwar ban-gaskiya, wadda za ku iya kashe dukkan kiban wutar mugun nan da ita; ku kuma dauki kwalkwalin ceto da takwabin Ruhu, wato maganar Allah.” Bari mu gan su a takaice,