✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makaman Yaki na Kirista (4)

Allah Ya sake kawo mu wannan lokacin bincike a cikin wannan mako; idan Allah Ya yarda za mu ci gaba da koyarwar da muke kai…

Allah Ya sake kawo mu wannan lokacin bincike a cikin wannan mako; idan Allah Ya yarda za mu ci gaba da koyarwar da muke kai tun mako uku da suka gabata. A makon jiya mun soma magana ne a kan duniya, maganar Allah tana koya mana cewa, duk abin da zai dauke hankalin mutum daga tsoron Allah, dole ne mu guje shi, ba abin alheri ne ba ko kadan. Abin da muke gani ke nan a cikin wannan duniya; abubuwan da suke gaba da nufin Allah cikin rayuwar dan Adam. A cikin Littafin 1Yohanna 2: 15 – 17, maganar Allah tana cewa, “Kada ku yi kaunar duniya ko abubuwan da ke cikin duniya, idan kowa ya yi kaunar duniya; kaunar Uba ba ta cikinsa ba. Gama dukan abin da ke cikin duniya da kwadayin jiki da sha’awar idanu da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne. Duniya ma tana wucewa duk da sha’awatata, amma wanda ya aikata nufin Allah ya zauna har abada.”
Ina so mu san abu guda muhimmi; cewa wannan Yaki na Ruhaniya yana somawa ne daga cikin tunanin mutum,  kamar yadda maganar Allah ta koya mana cikin Littafin 2Korinthiyawa 10:3-6, a wurin maganar Allah tana koya mana cewa: “Gama ko da muna tafiya cikin jiki, ba mu yi yaki bisa ga jiki ba, (gama makaman yakinmu ba na jiki ba ne), amma masu iko ne gaban Allah da za su rushe wurare masu karfi; muna rushe zace-zace da kowane madaukakin abu wanda aka daukaka domin gaba da sanin Allah, muna komo da kowane tunani cikin bauta ga biyayyar Kiristi; muna shiri fa mu dauki fansa bisa dukan kangara, sa’ar da biyayyarku ta cika.”
Mu gane wannan sosai, yakin Ruhaniya daga zuciya take somawa, a cikin tunaninmu na yau da kullum; idan maganar Allah ta ce kada mu kaunaci duniya ko kuwa abin da ke cikinta, abin nufi a nan shi ne, kada mutum ya kallafa ransa a cikin kayan da zai samu a cikin wannan duniya, domin babu guda daya da zai dauwama.
Mene ne yakan sa mutum ya aikata wani abin da bai gamsar da Ubangiji Allah?  Mu dauki misali, kafin wani ya yi zamba, sai ya yi tunani a kan abin da zai aikata, sai ya tantance cikin zuciyarsa ko yana so ya aikata abin da yake tunani a kai ko kuwa a’a, idan ya yanke shawara cikin zuciyarsa game da abin da yake tunani a kai, a lokacin zai iya aikata abin da ya yi niyya. Babu dole a ciki ko kadan, ra’ayinsa ne, abin da Shaidan yake yi a koyaushe shi ne, ya kawo wa mutum shawara, shawarar da Shaidan zai kawo kuwa a koyaushe, ba shawara ce ta aikata wani abin da zai gamsar da Allah ba ne ko kadan, amma shawara ce ka aikata wani abin da zai saba wa umarnin Allah Ubangijinmu. Wajen yakin shi ne: idan har ka yarda da ra’ayin Shaidan ka ci gaba ka aikata abin da Allah ba Ya so, Shaidan ya ci nasara. Idan kuwa ka gane da wuri cewa wannan shawara ce daga wurin Shaidan da kansa, sai ka yi tunani a cikin zuciyarka, sai ka yarda cikin zuciyarka cewa ba za ka yi ganganci da umarnin Allah ba, sai ka ki ka aikata wancan abin da Shaidan yake so ka yi, to ka ci nasara ke nan bisa Shaidan. A cikin zuciya ne mutum yakan ci nasara ko kuma a ci nasara bisansa.
Idan muka sake komawa wurin da muka yi karatu a cikin 1Yohanna 2: 3-6, za mu ga irin bayanin da ke akwai, idan muka lura sosai, za mu ga dalilin da yakan sa mutane su yi abin da suke yi, idan suka samu kansu a matsayin manya. Shugabanci ko na kasa baki daya, ko na jiha, ko kuwa na karamar hukuma, me ya sa mutane da yawa da Allah Ya ba su amanar rikon shugabancin jama’a ko al’umma sukan ci amanar mutanen Allah ne da kanSa Ya damka musu su yi mulki a bisansu? Halin sha’awa irin ta mutumtaka da sha’awar ido da alfarmar banza, ba za su taba gamsar da Ubangiji Allah ba ko kadan. Abin da Shaidan yakan yi shi ne, da yake ya san Allah ba Ya son irn wannan hali, shi zai shuka irin rashin jin tsoron Allah a cikin zuciyar mutane, sai mu ga suna nuna wadansu halayen da ba ka taba zata suna da su ba. Za ka ga wani da kake gani kamar yana jin tsoron Allah sosai, amma idan ka kai shi inda misali akwai kudi mai dimbin yawa, sai ka ga ya manta da alkawarin da ya dauka a gaban Allah da mutane a ranar da an rantsar da su. Abin da zai shigo musu a tunani shi ne yaya zan yi in samu kudi sosai a wannan lokaci kafin in sauka daga karagar mulki? A yau cikin wannan kasa ana tuhumar mutane da yawa game da kudaden da suka salwantar cikin shekaru da dama da suka gabata. Dalili daya ne kawai, shi ne lokacin da Shaidan ya kawo musu shawara, sun karba, babu wanda ya tilasta su. Da sonsu ne suka ki jin muryar Allah, suka zabi su saurari muryar Iblis. Gaskiyar ita ce masu iya magana sun ce akwai ranar kin dillanci, kafin mutum ya yarda ya bi nufin Allah ko kuwa nufin Shaidan. Akwai lokacin jayayya cikin zuciya, wani gafe yana cewa kada ka yi, wani gefen kuma na faman cewa ka ci gaba kawai babu abin da zai faru. Idan har mun iya kame kanmu, muka saurari muryar Ubangiji Allah Wanda Yake magana da mu cikin Littafi Mai tsarki, Littafin Rai, ba za mu taba yin kuskure ba. Kada mu bar Shaidan ya toshe mana kunne har da ba za mu iya sauraron Allah ba. Mu lura, wannan yaki daga tunani ne yake somawa. Duk zunubin dan Adam zai aikata, mafarinsa zuciya. Haka kisa ko zina ko sata ko cin hanci ko cin amana ko kishi ko son kai ko bautar gumaka da dukan sauran zanubai wadanda za ka iya tunawa, daga zuciya ne suke farawa. Ya kamata mu yi hankali da abin da ke a cikin zuciyarmu. Idan Allah Ya yarda za mu soma bincike a kan yaya za mu yi wannan yaki da kuma irin makaman da za mu yi yakin nan da su. Ubangiji Allah Ya bishe mu Ya kuma tsare mu daga dukan jarabawar Shaidan, amin.