Majalisun Dokokin Jihohin Najeriya sun yi watsi da kudurin bai wa kananan hukumomin kasar ’yancin cin gashin kai da majalisar tarayya ta mika musu don amince wa.
Kudurin dai da karin wasu guda tara ne da majalisar ta yi wa kwaskwarima daga dokokin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, a watan Maris.
- Buhari ya nada Solomon Arase Shugaban Hukumar Harkokin ’Yan Sanda
- Yawaita yin azumi zai iya haifar da ciwon koda – Shugabar NAFDAC
Majalisar dai ta ce 44 daga ciki sun samu sahalewar Majalisar Dattijai da ta Tarayya tun a watan, kuma sun mika su ga jihohin ne domin amincewa da su, kafin mika su ga Shugaban Kasa ya zartar da su.
Kudurorin dai na bukatar kashi biyu cikin uku na kuri’un majalisun jihohi, wanda ya yi daidai da jihohi 24 daga 36 da kasar ke da su.
Yayin zaman majalisar na ranar Talata, dan Majalisar Dattijai daga Jihar Delta, Omo Agege ya ce jihohi 27 cikin 36 sun aike wa majalisar sakamakon zaman nasu kan kudirorin da majalisar ta mika musu.
Omo-Agege, wanda Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti) ya gabatar da kudirin nasa, ya ce kudirori 35 daga ciki, sun samu amincewar 24 daga cikin jihohin, tara kuma ba su wuce ba.
Daga cikin kudurori 35 da majalisun jihohi suka amince da su har da na cin gashin kai a harkokin kudi na majalisun jihohi da na bangaren shari’a, sai na rage wa gwamnatin tarayya karfi da kara wa gwamnatin jiha a samun damar ginawa da sarrafa filayen jiragen sama, da gidajen yari, da layin dogo hadi da na’urorin wutar lantarki.
Sauran sun hada da bai wa majalisun ikon yi wa shugaban kasa da gwamnoni kiranye, da sanya wa’adin mika sunayen ministoci da kwamishinoni, da lokacin gabatar da kasafin kudin, hadi da kuma raba ofishin Atoni janar na kasa ko na Jiha da na minista ko kwamishinan shari’ a.