✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Wakilai ta yi watsi da kudirin kafa dokar haramta Acaba

Yallemen ya nuna cewa muddin aka haramta sana'ar acaba za a fuskanci karuwar matsaloli a kasar.

Majalisar Wakilai ta taka wa wani kudiri da ke neman kafa dokar haramta sana’ar acaba a fadin kasa burki.

Yayin zamanta na ranar Talata, dan majalisar Jigawa na jam’iyyar APC, Abubakar Yallemen ne ya gabatar da kudurin, inda ya bukaci su yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da shirin da take yi na haramta sana’ar acaba a fadin kasar.

Dan majislisar ya bukaci a tabbatar da an samar da shirye-shiryen da za su taimaka wajen rage wa ‘yan kasa radadin haramta acaba kafin daukar matakin hanawa.

Ya kara da cewa, idan ya kama a haramta sana’ar ta acaba, ya zamana hakan ya shafi yankunan kananan hukumomin da suke fama da ‘yan ta’adda da kuma harkokin hakar ma’adinai ne kadai.

Sa’ilin da yake gabatar da kudirin nasa ga majalisar, Yallemen ya nuna cewa muddin aka haramta sana’ar acaba hakan zai jefa rayuwar miliyoyin ‘yan Najeriya cikin halin rashin aikin yi, wanda a cewarsa hakan zai zama karin matsala ga kasar da ke fama da talauci da kuma zaman kashe wando.

Ya ce wajibi ne yayin da ake shirin haramta acaba a matsayin wani mataki na magance matsalar tsaro, a kum yi la’akari da walwalar ‘yan kasa kamar yadda Sashe na 14(2)(b) na Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya tanadar.

Sai dai kuma, Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Honorabul Ahmed Wase, ya jaddada bukatar ‘yan majalisar su mara wa Gwamnatin Tarayya baya wajen shawo kan matsalar tsaron da ta addabi kasa.

(NAN)