Shugaba Buhari ya kira zaman gaggawa na Majalisar Tsaron Kasa, inda ake sa ran tattauna kan yanayin da tsaro yake ciki a fadin Najeriya.
Zaman da ya gudana a Fadar Shugaban Kasa na zuwa ne washegarin wata ganawar Shugaban Kasar da Ministan Tsaro, Babban Hafsan Tsaro da Babban Hafsan Sojin Kasa, inda suka yi alkawarin inganta tsaron kasar.
A baya-bayan nan matsalar tsaro ta yi kamari a sassan Najeriya inda kungiyar a-waren Biafra ta IPOB ta yawaita kai hare-hare a kan gine-ginen gwamnati da jami’an tsaro a yankin Kudu maso Gabas.
A ’yan kwanakin da suka wuce, Gwamnatin Tarayya ta dakatar da dandalin sa da zumunta na Twitter daga aiki a Najeriya saboda zargin Twitter da kawar da kai kan kalaman tsana da neman tayar da husuma da IPOB ke yi ta kafar.
A yankin Arewa kuma matsalar masu garkuwa da mutane da kungiyar Boko Haram da rikicin manoma da makiyaya da na kabilanci sun dade ana fama da su.
Mafi daukar hankali a baya-bayan nan shi ne garkuwa da sama da kananan yara dalibai sama da 100 a wata makarantar Islamiyya a Jihar Neja, inda ’yan bindiga suka mayar tamkar cibiyar ayyukansu.
A wasu yankunan kuma ana fama da rikice-rikicen kabilanci da na manoma da makiyaya da ke kara ci wa kasar tuwo a kwarya.
Zaman na ranar Talata ya samu halarcin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ministan Tsaro da Minstan Harkokin Waje da sauransu.
Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Manyan Hafsoshin Tsaro, Shugaban ’Yan Sanda da takwarorinsa na Hukumar Leken Asiri da na Hukumar Tsaro ta DSS su ma sun halarci zaman.