Majalisar Tsaro ta Najeriya ta yi kira ga wadanda suka kirkiro Rundunar Tsaro Mai Yaki da Yaduwar Manya da Kananan Makamai ta Najeriya (NATFORCE) da su gaggauta rusa ta.
Majalisar ta ce in kuwa ba su yi haka ba nan da wani dan lokaci, jami’an tsaro za su tilasta musu yin haka nan ba da jimawa ba.
Ministan Al’amuran Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, lokacin da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa, bayan kammala taron majalisar wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadarsa da ke Abuja.
Yanzu haka dai kudurin neman kafa hukumar na gaban Majalisar Dokoki ta Kasa a daidai lokacin da yake cin karo da suka daga masana harkokin tsaro.
Aregbesola ya ce majalisar ta koli a kan harkokin tsaro ta kuma jinjina wa jami’an tsaro kan ayyukansu na magance matsalolin tsaro a Najeriya.
Ya ce gwamnati mai ci na fatan kawo karshen ilahirin matsalolin Najeriya nan da watan disamba mai zuwa.
“Mun gamsu da rawar da jami’an tsaro, musamman ’yan sanda suka taka yayin zabukan gwamnonin da aka gudanar a jihohin Ekiti da Osun.
“Kazalika, muna nuna damuwa da wasu hukumomin tsaro da aka kafa ba bisa ka’ida ba da ke yin sojan gona. Wacce ta fi damun majalisar ita ce rundunar da aeke kira da NATFORCE.
“Majalisar Tsaron ta yanke shawarar cewa ba ta kan ka’ida, kuma ya kamata ta gaggauta rusa kanta da kanta, saboda mun ba jami’an tsaro damar rusa ta da ma wata runduna da ba ta kan doron doka,” inji Aregebesola.