Majalisar Dokokin Jihar Ondo ta dakatar da mataimakin shugaban Majlisar, Irouju Ogundeji da bisa zargin rashin da’a.
Zauren majalisar ya kaure da hayaniya sakakamon dakatar da Irouju da kuma Hon. Adewale Willams bisa zargin tsaurin ido a zamanta na ranar Laraba.
Mutanen biyu na daga cikin ‘yan majalisar guda tara da a ranar Talata suka kalubalanci yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Agboola Ajayi.
14 daga cikin ‘yan majalisar ne neman tsige mataimakin gwamnan ne saboda zarginsa da saba ka’idojin aiki da almubazaranci da kuma wasa da aiki.
Majalisar na bukatar kashi biyu cikin uku na mambobinta wato mutum 17 kafin ta iya tsige mataimakin gwamnan.