Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta dage zaman da ta shirya yi na neman Muhuyi Magaji Rimin Gado ya bayyana gabanta kan zargin aikata ba daidai ba da gwamnatin jihar ke yi masa.
Bayanai sun ce Majalisar ta dage zaman ne har sai Baba ta gani.
- Dalilin da APC ta fadi zaben wasu jihohi a 2019 —Buhari
- An bayyana Gwarazan Gasar Rubutattun Wakokin Hausa
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, wannan na zuwa ne bayan rashin bayyanar Muhuyin a gaban kwamitin a yau kamar yadda aka bukata.
A cewar lauyansa, bai sami amsa gayyatar ba saboda rashin lafiya da yake fama da ita, wanda yake ganin likita a wani asibiti a Abuja.
Sannan ya ce kawo yanzu ba a bai wa Muhuyi jerin tuhume-tuhumen da ake yi masa ba.
Tun a farkon watan Yulin nan ne Majalisar ta dakatar da Muhuyi da ke zaman Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin hanci da Rashawa (PCACC).
Majalisar ta dakatar da shi ne saboda kin karbar sabon akantan da Akanta Janar na Jihar Kano ya tura wa hukumar.
Dakatarwar, wacce ta fara aiki nan take, ta biyo bayan samun takardar korafi da Majalisar ta yi daga Ofishin Akanta Janar din ne a kan lamarin.
Bayan mako guda da dakatarwar ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar, ya nada Barista Mahmoud Balarabe, a matsayin mukaddashin Shugaban Hukumar (PCACC).