Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da Kudurin Dokar Masarautu ta 2020, da ta samar da karin sarakunan yanka hudu Jihar.
Zaman Majalisar da Shugabanta, Abdulazeez Gafasa ya jagoranta ya amince da sauye-sauyen da aka yi wa dokar masarautun da ya kara yawan sarankunan yankan jihar daga daya zuwa biyar.
- Saura kiris a rufe daukar sabbin ma’aikata 774,000
- Mutum shida ‘yan gida daya sun mutu a ambaliyar Kebbi
A shekarar 2019 ne Majalisar ta amince da kafa sabbin masarauta hudu a Jihar da suka hada da Gaya, Karaye, Rano da Bichi, baya ga masarautar Kano da a baya ita ce kadai a fadin jihar.
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Kabiru Dashi ya ce gyaran fuskar da aka yi wa dokar ta tanadi cewa Sarkin Kano ne zai zama Shugaba Majalisar Sarakunan Jihar, wanda ya kawo karshen ce-ce-ku-ce game da batun karba-karbar Shugabancin Majalisar Sarakunan.
“Sabuwar dokar ta kara yawan masu zaben sarki daga hudu zuwa biyar domin bayar da damar zabe na adalci a duk sadda bukatar zaben sabon sarki ta taso.
“Kara yawan masu zabar sarki zuwa mutum biyar na nufin za a samu adalci a zaben. Sabuwar dokar ta kuma kayyade kwana uku a matsayin wa’adin zaben sabon sarki”, kamar yadda ya bayyana.
Dokar ta kuma sauya saunana Majalisar Hakimai zuwa Majalisar Sarakuna.