✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Gombe ta jajanta kan gobarar Majalisar Katsina

Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta jajanta wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Tasi’u Maigari, bisa iftila’in gobarar da ta cinye wani bangare na zauren majalisar.…

Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta jajanta wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Tasi’u Maigari, bisa iftila’in gobarar da ta cinye wani bangare na zauren majalisar.

Sakon da Babban Jami’in Yada Labarai na Majalisar, Abubakar Muhammad Umar, ya fitar, ta bayyana girgizar Majalisar da samun labarin gobarar, a daidai lokacin da al’ummar Katsina suke farfadowa daga gobarar Babbar Kasuwar Katsina.

Sakon ya ce Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Abubakar Muhammad Luggerewo, ya ce Katsinawa mutane ne masu tawakkali, don haka su dauki gobarar a matsayin kaddara, su kuma roki Allah Ya ba su hakurin jure iftila’in.

Daga karshe ya tabbatar wa da Majalisar ta Katsina da cewa za su ci gaba da taya su addu’ar Allah Ya kare sake aukuwar hakan, Ya Kuma mayar musu da mafi alherin asarar da suka yi.