✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu karɓo rancen Naira tiriliyan 1.77 daga ƙetare

Majalisar Dattawa ta amince Shugaba Bola Tinubu ya ranto naira tiriliyan 1.77 kimanin dala biliyan 2.2 daga ƙetare. Matakin dai ya biyo bayan nazari tare…

Majalisar Dattawa ta amince Shugaba Bola Tinubu ya ranto naira tiriliyan 1.77 kimanin dala biliyan 2.2 daga ƙetare.

Matakin dai ya biyo bayan nazari tare da amincewa da rahoton Kwamitin Majalisar kan basussukan cikin gida da waje, wanda Sanata Aliyu Wamakko da ke wakiltar Sakkwato ta Arewa ya jagoranta.

A ranar Talata ce Shugaba Tinubu ya aike wa Majalisar Dokokin Tarayya wasiƙar neman sahalewa ya ranto bashin Naira tiriliyan 1.77 a matsayin sabon tsarin rancen aiwatar da Dokar Kasafin Kuɗin bana.

Wasiƙar Shugaban ta ce za a yi amfani da rancen wajen cike giɓin Naira tiriliyan 9.7 da ke cikin Kasafin Kuɗin na bana.

Haka kuma, Shugaba Tinubun ya aike da matsakaicin kasafin da za a kashe tsakanin 2025 da 2027 ga majalisar tare da kudirin neman yin garambawul ga shirin tallafa wa al’ummar kasar, da nufin mayar da kudin bayanan ‘yan kasa ya zama abinda Gwamnatin Tarayya za ta riƙa amfani da shi wajen aiwatar da shirye-shiryenta na ba da tallafi.

Hakan na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan Babban Bankin Najeriya ya bayyana cewar gwamnatin ƙasar ta kashe dala biliyan 3.58 wajen biyan basussukan da ake binta a ƙetare a watanni 9 na farkon shekarar 2024 da muke ciki.