Majalisar Dattawa ta amince da kasafin kudin 2020 na Naira tiriliyan 10.801 da aka yi wa gyaran fuska.
Majalisar ta kara biliyan N292 a kan sabon kasafin tiriliyan N10.509 da Shugaba Buhari ya yi wa gyaran fuska.
A watan Disamban 2019 Majalisar ta amince da kasafin 2020 na Naira tiriliyan 10.594 wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu.
Daga baya Gwamantin Tarayya ta rage yawan kasafin saboda karyewar farashin mai a duniya da kuma raguwar kudaden shigan da kasar ta yi hasashen samu a 2020, sakamakon annobar COVID-19.
- Yadda Boko Haram ta zama masana’anta —Ahmad Lawan
- Mun sanya aikin gyaran hanyar Jos zuwa Kaduna a kasafin kudin bana – Maitala Jingir
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya tabbatar da amincewarsu da sabon kasafin bayan karbar rahoto daga Shugaban Kwamintin Kasafi na Majalisar, Sanata Barau Jibrin.
Ahmed Lawan ya bukacin kwamitocin Majalisar da su yi tsaye a aikinsu na sa ido kan yadda ake aiwatar da ayyukan da aka ware wa kudade a kasafin.
Tun da farko a ranar Laraba Majalisar Wakilai ta amince da sabon kasafin da bangaren zartarwa ya gabatar.