✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Amurka ta tsige Shugaba Donald Trump

‘Yan majalisar wakilan Amurka sun jefa kuri’ar da ta tabbatar da tsige Shugaba Donald Trump, bisa wasu laifuka guda biyu da suka gabatar. Shugabar majalisar…

‘Yan majalisar wakilan Amurka sun jefa kuri’ar da ta tabbatar da tsige Shugaba Donald Trump, bisa wasu laifuka guda biyu da suka gabatar.

Shugabar majalisar wakilan Nancy Pelosi ta bayyana cewa ‘yan majalisa 230 sun goyi bayan tsige shugaban yayin da 197 suka ki amincewa.

Laifin Mista Trump na farko shi ne kokarin tursasa shugaban Ukraine da ya binciki abokin hamayyarsa, a zabe mai zuwa, kuma tsohon mataimakin shugaban kasar, Joe Biden.

Laifi na biyu kuwa ya hada da kokarin kawo wa majalisa tarnaki. Mista Trump a yanzu ya zamo shugaba na uku da aka taba tsigewa.

Sai dai Shugaba Trump ya mayar da martanin ne a wani gangami a Michigan, yana nuni da cewa wannan tsigewar ko a jikinsa.

Rahoton BBC