✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa za ta binciki abin da ya haddasa tsayawar jirgin kasan Legas a daji

Hukumar Sufurin Jiragen Kasa, ta ce mai ne ya kare wa jirgin a tsakiyar daji.

Majalisar Wakilai ta kuduri aniyar  bincike kan abin da ya haddasa tsayuwar wani jirgin kasa a dokar daji baya ya dauko fasinja daga Legas zai kai su Ibadan.

A satin da ya gaba Aminiya ta rawaito yadda aka rika yada hotunan jirgin a kafafen sadarwa, inda aka nuna jirgin kasa ya tsaya a kan hanyar Legas zuwa Ibadan, ga kuma fasinjoji sun yi cirko-cirko, ana kokarin zuba mai.

Hukumar Kula da Jiragen Kasa (NRC) ta ce mai ne ya kare wa jirgin, lamarin da ya fusata majalisa inda ta kira faruwar lamarin da rashin iya aiki.

Abubakar Yunus, daya daga cikin ’yan Majalisar Wakilai, ya bayyana cewa za a gudanar da binciken ne duba da irin kudaden da aka narka a harkar sufurin jirgin kasa.

“Wannan wani abu ne da ba a saba gani ba, kuma ganin cewa an ciyo bashin makudan kudade, ga shi kuma an fara samun irin wadannan matsaloli.

“Gara a yi bincike,  don me jirgin kasa zai tsaya bayan ya taso daga tasharsa? Rashin mai ne ko dai sakaci ne har mai ya kare bai kai inda zai je ya gama zirga-zirgarsa ba,” cewar Honarabul Yunus.

Ya bayyana cewa ana sa ran kwamitin da aka kafa kan lamarin zai kammala binciken cikin mako biyu ya gabatar da rahoton bincikensa.

Har wa yau, daga cikin abin da kwamitin zai bincika har da zargin boye tikiti da ake wa ma’aikatan Hukumar Sufurin Jiragen Kasan domin sayarwa da tsada ga masu kudi.

Wannan ba shi ne karo na farko da jirgin kasa ke tsayawa a daji ba ba a Najeriya.

Ko a shekarar da ta gabata ’yan bindiga sun kai wa wani jirgin kasa hari wanda ya sa shi tsayawa tsakanin Abuja zuwa Kaduna.

Kazalika, jirgin kasa ya sha lalacewa a cikin daji lamarin da ya sanya fasinjoji jiran kusan awa biyu kafin isowar wani jirgin ya kwashe su.