✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta yi watsi da yarjejeniar Samoa

Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar sai an warware duk sarkakiyar da ke tattare da ita.

Majalisar Wakilai ta watsi da arjejeniar Samoa da Gwamnatin tarayya ta rattaba hannu a kai.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin ta warware yarjejeniyar sai an kammala gudanar da bincike kan duk sarkakiyar da ke tattare da ita.

Majalisar ta cimma wannan matsaa ne a ranar talata, sakamakon dambarwar da ta dabaibaye yarjejeniyar.

Mambobi 88 na majalisar ne suka goyi bayan kudurin da ke neman gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar Samoa har sai an warware duk wasu batutuwan da ke haifar da ce-ce-ku-ce.

Da yake gabatar da kudirin a ranar Talata, Honorabul Aliyu Madaki, ya ja hankali cewa akwai yiwuwar wata a cikin batun da ke nuna “daidaitan jinsi” a cikin yar jejeniyar.

Daga karshe Majalisar ta umarci kwamitocinta da su binciki abin da yarjejeniyar ke kunshe da shi da suka haifar da ce-ce-ku-ce.

Takaddama dai ta kunno kai kan yarjejeniyar Samoa da gwamnatin tarayya ta rattaba hannu da kungiyar Tarayyar Turai, inda da dama suka nuna rashin jin dadinsu da zargin gwamnatin ta amince da lamarin  ’yancin ’yan madigo da ’yan luwadi da ’yan daudu, da kuma auren jinsi.

Yarjejeniyar Samoa ta haifar da ce-ce-ku-ce tare da zargin neman ’yancin aruen jinisi, wanda hakan ya saba wa dokar hana auren jinsi ta shekarar 2014 da shugaba Goodluck Jonathan ya sa wa hannu.

A taron manema labarai a ranar Asabar, Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu; Tare da takwaransa na Ma’aikatar Yada Labarai, Mohammed Idris, ya ce Najeriya ba za ta kulla wata yarjejeniya da ta saba wa kundin tsarin mulki ba da kuma addini da al’adun al’ummar kasarta.

Bagudu ya ce Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ne domin bunkasa samar da abinci, da habaka tattalin arziki da sauran muhimman fannoni.

A watan Nuwamban da ya gabata ne kungiyar Tarayyar Turai da kasashenta 27 da kasashe 79 na kungiyar kasashen Afirka, Caribbean da Pacific (OACPS) suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya a Apia, babban birnin tsibirin Samoa.

Don haka, an kiran ta da ‘Yarjejeniyar Samoa’.