✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta yi barazanar kama Buba Marwa da Monguno

Barazanar ta biyo bayan kin amincewarsu su amsa gayyatar majalisar.

Majalisar Dattijai ta yi barazanar ba da sammacin kama Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Buba Marwa da Mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno.

Barazanar ta biyo bayan kin amincewa su amsa gayyatar da majalisar ta yi musu ta bayyana a gabanta.

Ofishin Babban Mai Binciken Kudi na Kasa ne dai ya yi wa ofisoshin biyu wasu zarge-zage a wani rahotonsa na 2016, wanda kuma Kwamitin Asusun Gwamnati na majalisar yake bincike a kai.

NDLEA na fuskantar tambayoyi 11 da ake bukatar ta amsa, wadanda suke da alaka da karkatar da kudaden da yawansu ya kai kusan Naira miliyan 467.

Rahoton binciken dai ya nuna cewa an aikata laifin da ake zargi ne a shekarar 2015, kafin Buba Marwa ya fara shugabancin hukumar.

Shi kuwa Ofishin Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro ana tuhumarsa ne da karkatar da kudin da adadinsu ya kai kusan Naira biliyan uku da rabi ne wadanda aka ware domin Hukumar Bunkasa Kirkira ta Kasa (NADDC), domin sayo wa jami’an sojoji motoci.

Sanata Matthew Urhoghide, wanda shi ke jagorantar kwamitin majalisar da ke binciken zarge-zagen ya ce jami’an biyu sun yi biris da gayyatar da majalisar ta yi musu a lokuta daban-daban don jin ba’asi a kansu.

Sanatan, ya sha alwashin cewa majalisar za ta yi amfani da dukkan ikon da Kundin Tsarin Mulki ya ba ta wajen tilasta musu su bayyana a gaban nata.