✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta soke bambanci tsakanin masu digiri da masu HND

Yanzu dai dokar na a jiran sahalewar Shugaban Kasa kafin ta fara aiki.

Majalisar Dattijai a ranar Laraba ta amince da kudurin dokar haramta nuna bambanci tsakanin masu takardar shaidar digiri da masu babbar diflomar, wato HND. 

Hakan ya biyo bayan la’akarin da majalisar ta yi da rahoton kwamitocinta kan Ayyyukan Gwamnati da Kamfanoni da kuma na Manyan Makarantu da na asusun TETFUND. 

Shugaban hadin gwiwar kwamitocin, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce, “Kafa dokar kawar da bambanci tsakanin masu shaidar takardar digiri da masu babbar diflomar HND a Najeriya, ko shakka babu zai bude kofar daga likkafar masu HND.

“Sannan zai taimaka wajen kawo daidaito tsakaninsu da takwarorinsu a sauran manyan makarantun kasar nan,” inji Shekarau.

Ya kara da cewa soke bambancin zai kuma taimaka gaya ta fuskar inganta aiki da tabbatar da adalci tare da bayar da gudunmawa sosai daga masu karatun HND a ma’aikatun gwamnati da kamfanoni.

Shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya ce sahale kudurin dokar da majalisar ta yi zai kara wa daliban da suka halarci kwalejojin fasaha karsashi.

Don haka ya bukaci ma’aikatun gwamnatin da masu zaman kansu da su tabbatar da sun yi aiki da tanadin dokar da zarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba mata hannu.