Majalisar Dattawa jiya ta zartar da kudurin soke asusun rarar man fetur wanda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa a shekarar 2004.
Amincewar ta biyo bayan kudurin da ’yar majalisa Rose Oko ta jam’iyyar PDP daga jihar Kuros Riba da wasu mutum 44 suka goyi baya wanda aka yi masa lakabin “Asusun rarar man fetur, ya saba wa doka”.
A yayin da Oko ta nemi da a dakatar da asusun, sai Sanata Muhammaed Hassan na jam’iyyar PDP daga jihar Yobe ya gabatar da kudurin a soke asusun inda daga bisani ’yan majalisar suka goyi bayansa.