Majalisar Tarayya ta kai karar Babban Bankin Najeriya (CBN) da kamfanin NNPC da Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA) wurin Shugaba Buhari kan kin amsa gayyatar da ta yi musu.
CBN da NNPC da NPA da daga cikin hukumomin Gwamnatin Tarayya da majalisar ke neman su domin su yi bayani game wasu kudade da bayanai da suka shafe su masu ayar tambaya a kansu.
Sauran hukumomin da Majalisar ke da bincika su ne Hukumar Agaji ta Kasa da kuma Asusun Daidaito na Albarkatun Mai (PEF).
Kwamitin kwamitin binciken ayyukan gwamanti na Majalisar Wakilai Wole Oke ya bukaci Shugaban Kasa ya umarce su da su hallara domin amsa tambayoyin majalisar cikin kawana bakwai.
Zaman Kwamitin ya umarci akawunsa da ya aike da sakon ga shugaban kasa ta hannun Sakataren Gwamnatin Tarayya da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.