Majalisar Wakilan Rasha ta amince da sabuwar dokar da ta haramta duk wani yunkurin yada farfagandar da ke goyon bayan auren jinsi a sassan kasar.
Sabuwar dokar wadda a ranar Alhamis aka kada wa kuri’a ba tare da hamayya ba, Mosow ta tsaya kai da fata game matsayarta na haramta duk wata alakar auratayya da ta saba wa yadda dan adam ya gada tsawon shekaru a ban kasa.
- Dalibi ya kashe kansa saboda gaza mallakar wayar salula ta N50,000
- Matashi zai yi zaman wakafi saboda satar wayar salula a Ekiti
Da ya ke jawabi game da sabuwar dokar, Kakakin Majalisar Wakilan ta Rasha Vyacheslav Volodin, ya ce akwai hukunci mai tsauri kan duk wanda aka samu da laifin wanda ya saba da halittar dan adam.
Majalisar ta Rasha cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Telegram, ta ce sabuwar dokar za ta kange al’ummar kasar musamman masu tasowa a nan gaba daga mummunar akidar wadda Amurka da kasashen Turai ke son karfafata a Duniya.
Dokar dai na bukatar goyon bayan Majalisar Dattijai da kuma sanya hannun shugaba Vladimir Putin gabanin fara aiki da ita tare da hukunta wadanda aka samu da wannan dabi’a ko kuma farfagandarta.