✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta gayyaci Lai Mohammed kan dakatar da Twitter

Ministan Sadarwa zai bayyana a gaban Majalisa kan dakatar da Twitter a Najeriya

Majalisar Tarayya ta bukaci Ministan Sadarwa, Lai Mohammed ya bayyana a gabanta kan dakatar da dandalin sada zumunta na Twitter a Najeriya.

Majalisar Wakilai ya bayar da umarnin gayyato ministan ne domin ya yi bayani kan hikimar matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na dakatar da Twitter a kasar.

Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, ya sanar da haka ne a jawabinsa bayan dawowarta a safiyar Talata.

Ya umarci Kwamitin Sadarwa da Harkokin Shari’a na Majalisar da su tabbatar da umarnin cikin kwana 10.