✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rashin tsaro: Majalisa ta bukaci a dage kidayar 2021

Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnati ta dakatar da kidayar da aka shirya gudanarwa a bana.

Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kidayar jama’a da gidaje da aka shirya gudanarwa a bana.

Majalisar ta yi kiran ne bayan dan majalisa mai wakiltar Bosso/Paikoro dag Jihar Neja, Shehu Beji ya bayyana cewa matsalolin tsaro da sauransu za su shafi sahihancin alkaluman kidayar.

Ya ce matsalar rashin tsaro da ke barazana ga ka ’yan Najeriya ya sa yawancinsu kaura daga yankunansu, wanda zai yi illa ga nasarar da ake burin cimma da aikin.

A cewarsa, baya ga haka, su kansu jami’an kidayar babu tabbacin tsaron lafiyarsu a wuraren da za su gudanar da aikin a sassan kasar inda a wasu wuraren ake fama da rikice-rikice.