Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmee Lawan ya yi kira da a gurfanar tare da gudanar da shari’ar masu satar man fetur a kasar nan cikin gaggawa.
Shugaban ya yi kiran ne a wata ganawa da ya yi da shugabanin hukumomin tsaro na kasar nan a Abuja, a ranar Litinin.
- Yadda Majalisar Dattijai ta yi ban kwana da Saraki
- EFCC ta cafke Kakakin Majalisar Ogun a filin jirgin saman Legas
Shugaban majalisar ya jinjina wa jami’an tsaro a bisa namijin kokarin da suke yi a yakin da suke yi da ’yan ta’adda, a inda yawacinsu aka kame, wasu kuma da yawa aka kashesu.
Sannan ya ce irin wannan kokari ya kamata jami’an su yi irinsa a kan barayin mai na kasar, la’akari da yadda su ke zagon kasa ga tattalin arzikin kasar nan.
“Ina so in ga ana shari’ar wadanda aka kama da wannan laifin, saboda ta haka ne jam’a za su ga karfin doka, da yadda ta ke aiki kan duk wanda ya taka ta, komai girmansa,” inji Ahmed Lawan.
Shugaban ya kuma yi kira ga kotunan kasar nan da su daina jan kafa a shari’un da su ke yi na laifukan da su ka danganci satar mai, da kuma bayyana wadanda su ke durewa barayin gindi.