✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maiyuwa Ajantina ba za ta halarci Gasar Cin Kofin Duniya ba

kasar Ajantina tana cikin tsaka mai wuya inda ake ganin da kyar in za ta haye zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi…

kasar Ajantina tana cikin tsaka mai wuya inda ake ganin da kyar in za ta haye zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi badi a kasar Rasha.

kasar ta fada cikin wannan matsala ne bayan ta yi kunnen doki 1-1 da kasar benezuela a gasar share fage na neman hayewa gasar cin kofin duniya da suka yi a ranar Talatar da ta gabata.

Sakamakon ne ya sanya Ajantina ta kasance a matsayi na biyar a jerin kungiyoyin 10 da ke fafatawa da suka fito daga Kudancin Amurka kuma kasashe hudun da ke sahun farko ne za su haye gasar cin kofin duniya yayin da wacce ta zama ta biyar sai ta buga wasan cancanta (play-off).

Kawo yanzu Ajantina ta hada maki 24 ne daga wasanni 16 kuma saura wasanni biyu a kammala wasannin share fagen.

Ana sa ran kasar da ta kasance ta biyar za ta fuskanci Newzealand ne wacce ta fito daga yankin Osheniya (Ocenia) a wasan neman cancantar hayewa gasar cin kofin duniya (play-off) da za a yi gida da waje.