An sako tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho na Najeriya (PRTT) Abdulrashid Maina daga gidan yari bayan shafe wata tara a gidan yarin Kuje.
“Wannan abu ne mai kyau a garemu domin za mu samu damar shiryawa da kyau domin kare kanmu a gaban kotu. Yanzu za mu tattauna yadda ya kamta kan lamarin”, inji Adeola Adedipe lauyan Maina.
Tun wata Oktoban 2019 Maina da kamfaninsa, Common Input Property and Investment Ltd. da kuma dansa suke tsare bayan kotun Mai Shari’a Okon Abang ta bayar da belinsu.
A watan Yuni lauyansa Joe Gadzama ya ce Sanata Ali Ndume ya amince ya tsaya wa Maina a matsayinsa na dan Majalisa mai ci, kamar yadda kotun ta shardanta.
Ndume ya ce ya yi hakan ne a matsayin wakiltar mazabar Maina ta Borno ta Kudu domin wanda ake zargin ya samu damar kula da lafiyarsa wadda ke cikin matsala.
Ana zargin Maina da aikta laifi 12 masu alaka da safarar haramtattun kudade amma ya musanta zarge-zargen.