✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’ikatan Sahad da aka kora sun koka game da halin da suke ciki

Ma’aikatan katafaren kantin sayar da kayayyakin masarufi na Sahad Stores da ke Kano sun koka  kan halin da suka shiga sakamakon korarsu daga aiki bisa…

Ma’aikatan katafaren kantin sayar da kayayyakin masarufi na Sahad Stores da ke Kano sun koka  kan halin da suka shiga sakamakon korarsu daga aiki bisa zargin bacewar Naira miliyan 250 daga katin.

Ma’aikatan su 74 da suke aiki a kantunan Sahad da ke Titin Gidan Zoo da na Mandawari sun  ce rana tsaka suka samu bayanin cewa kamfanin ya sallame su ba tare da biyansu kudin sallama ba.

Ma’aikatan wadanda suka nemi a sakaya sunansu sun bukaci Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II su sanya baki a  wannan magana don ganin an mayar da su bakin aikinsu ko a biya su hakkokinsu.

Daya daga cikinsu ya ce “Yanzu a cikinmu akwai wadanda suka shafe shekara 12 suna aiki a wurin nan ba mu da wata sana’a daban. Ga shi muna da iyalai akalla a cikinmu ka samu wanda yake daukar nauyin mutum uku, wani ma iyalansa sun fi haka. To don Allah yaya za mu yi da rayuwa a wannan yanayi da ake ciki a kasar nan?”

Binciken Aminiya ya gano cewa ba dukkan ma’aikatan aka kora ba, akwai wadanda aka bari kuma ake ganin an bar su ne sakamakon wata alaka da ke tsakaninsu da Shugaban Kamfanin.

Tuni shagon na Sahad ya maye gurbin tsofaffin ma’aikatan da sababbi wadanda suke ci gaba da gudanar da aiki a katafaren shagon.

Duk kokarin Aminiya ta jin bakin Shugaban Shagon Alhaji Ibrahim Mijinyawa ya ci tura.

Sai dai wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa Kamfanin SAHAD ya dauki wannan mataki ne a kan ma’aikatan sakamakon bacewar Naira miliyan 250 daga  kamfanin.

“Gaskiya abin da ya faru da aka zo lissafin shekara ne aka tarar wasu kudade fiye da Naira mIliyan 200 sun bace don haka aka kore su,” inji majiyar.

A cewar majiyar Manajan Shagon ma wanda dan mai wurin ne shi ma an kore.

Kuma majiyar ta ce mamallakin shagon ya ce korarsu da ya yi shi ne mataki mafi sauki da ya dauka, domin a cewarsa da ya ga dama da zai yi kararsu gaban hukuma don su biya shi kudinsa.