Yarinyar nan mai shekara 12 da wani malamin Islamiyya ya yi wa fyade a watan Yunin 2021 a Ungwan Fantaro a Karamar Hukumar na Kachia ta Jihar Kaduna, ta haihu.
A lokacin dai, rahotanni sun ce malamin ya lokacin da take talla da cewa zai sayi kayan da take sayarwa na N200, amma ya ja ta dakuna ya yi mata fyaden.
- Yadda matsalar ruwan sha ta addabi Kanawa
- Kotu ta umarci Gwamnatin Najeriya ta bai wa mata kashi 35 na mukamai
Sai dai bayan wata uku, an gano yarinyar na dauke da juna biyu.
Daga bisani Ma’aikatar Kula da Walwalar Jama’a ta Jihar Kaduna, ta hannun wata kungiya mai zaman kanta mai suna Ummulkairi Foundation ta tsare ta ci gaba da kula da ita.
Kwamishinar Ayyuka ta Jihar, Hajiya Zainab Baba, ta tabbatar da haihuwar yarinyar ranar Alhamis.
“Yarinyar ta haifa da namiji sati uku da suka wuce kuma ina murna da yadda likitocin Asibitin Barau Dikko da ke Kaduna sun kula da ita har ta haihu da kanta maimakon a yi mata tiyata,” inji Kwamishinar.