Wata tsohuwa mai shekara 102 a duniya, Nonye Josephine Ezeanyaechi, wadda aka fi sani da ‘Mama Afirka’ ta ce ta shirya tsayawa takarar shugaban kasa, tunda matasa sun gaza shiga a dama da su.
Tsohuwar ta bayyana haka ne a gidan talabijin na kasa, NTA, yayin wata ziyara ta musamman da ta kai.
- Na amince zan dambata da Tyson Fury —Dillian Whyte
- Mun bai wa gwamnati da ASUU wa’adin mako daya su sulhunta —Kungiyar Dalibai
“Zan fito takarar shugaban kasa matukar matasa sun gaza fitowa a dama da su a siyasa.
“Idan kana da yara maza ko mata, yana da kyau ka horar da su ta yadda za su fi ka yin nasara a rayuwa,” inji ta.
Tsohuwar ‘yar asalin Karamar Hukumar Agwata a Jihar Anambra, ta kafa tarihin zama mutum mafi tsufa a Najeriya da ya ayyana kudurin tsayawa takarar shugaban kasa.
Tsohuwar, wadda ta sha gwagwarmaya a rayuwa, ta kafa kungiyoyi da dama tun daga gida har zuwa kasashen waje, wadanda suka hada da ‘Nigerians Diaspora Organization (Egbe Oma).
Da ya ke nasa jawabin Darakta-Janar na gidan talabijin na NTA, Yakubu Ibn Mohammed, ya jinjina wa tsohuwar kan irin rawar da ta taka a rayuwar mutane daban-daban a kasar nan.
Daraktan ya bayyana ‘Mama Afrika’ a matsayin jigo wadda Najeriya ke bukatar mutane irinta.